Dogara, da ‘Yan Majalisa 11 da su ka bar Jam’iyyar da ta taimaka masu lashe zaben 2019

Dogara, da ‘Yan Majalisa 11 da su ka bar Jam’iyyar da ta taimaka masu lashe zaben 2019

A siyasar Najeriya, ba sabon abu ba ne don ‘dan takara ko mai mulki ya sauya-sheka, har ana zargin ‘yan siyasar da cewa babu wata akida da su ke a kai.

Bayan zaben 2019, an samu wasu zababbun ‘yan majalisar tarayya da su ka tsere daga jam’iyyun adawa, kusan dukkaninsu sun koma APC mai mulki da rinjaye ne.

Wasu daga cikin wadannan ‘yan majalisa sun kafa hujja da rikicin cikin gida, wasu kuma ana zargin sun samu sabani ne da gwamnonin jihohin da su ka fito.

Legit.ng Hausa ta tattaro ‘yan majalisar da su ka koma APC a ‘yan kwanakin nan, ga su kamar haka:

KU KARANTA: Zaben 2023: Magoya baya su na tallata takarar Bola Tinubu

1. Yakubu Dogara

Ficewar Hon. Yakubu Dogara daga jam’iyyar PDP zuwa APC ya ba mutane mamaki. Tsohon shugaban majalisar wakilan ya samu sabani ne da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.

2. Ephraim Nwuzi

Honarabul Ephraim Nwuzi mai wakiltar mazabar Etche/Omuma a majalisar wakilai ya na cikin wadanda su ka sauya-sheka daga jam’iyyar mai mulki a Ribas, ya shigo tafiyar APC.

3. Chisom Dike

Wani ‘dan majalisa da jam’iyyar PDP ta rasa a jihar Ribas shi ne Honarabul Chisom Dike. Kamar dai Nwuzi, Dike mai wakiltar mutanen Eleme/Tai/Oyigbo ya zabi ya koma APC mai mulki.

4. Kolawole Lawal

A watan Oktoban bara ne Hon. Kolawole Lawal ya dawo jam’iyyar APC. ‘Dan majalisar na jihat Ogun ya yi watsi da jam’iyyar adawa ta APM da ta taimaka masa ya lashe zaben 2019.

5. David Abel

A shekarar da ta gabata ne David Abel ya rage wa PDP yawan ‘ya ‘ya a majalisa. ‘Dan majalisar mai wakiltar yankin Gashaka/Kurmi/Sardauna na jihar Taraba ya koma jam’iyyar APC.

6. Ali Datti Yako

Hon. Ali Datti Yako ya yi watsi da jam’iyyar PDP da ta ba shi nasara a zaben kujerar ‘dan majalisar Kiru da Bebeji. Ana zargin tun farko yarjejeniya aka yi tsakanin Datti Yako da APC.

7. Tajudeen Adeyemi Adegunsonye

A kwanakin baya aka samu labarin cewa Tajudeen Adeyemi Adegunsonye ya bar jam’iyyar SDP ya koma APC. ‘Dan majalisar tarayyar ya ce rikicin cikin gida ya addabi jam’iyyar SDP.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta shiga farautar wasu Gwamnonin jihohin PDP

8. Shiddi Danjuma

Hon. Shiddi Danjuma wanda yake wakiltar Ibi da Wukari na jihar Taraba a majalisar tarayya ya tsere daga jam’iyyar hamayya ta APGA, ya koma APC domin cin ma manufar siyasarsa.

9. Sam Onuigbo

A karshen shekarar da ta wuce ne Hon. Sam Onuigbo mai wakiltar yankin Ikwuano da Umuahia na jihar Abia a majalisar tarayya ya sauya-sheka daga PDP, ya koma jam’iyyar APC.

10. Abiola Peter Makinde

Dazu shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya bada sanarwar cewa Abiola Peter Makinde mai wakiltar yammaci da gabashin Ondo ya koma APC daga jam’iyyar ADC.

11. Blessing Onuh

A watan nan ne aka ji cewa ‘yar majalisar da ke wakiltar mazabar Otukpo/Ohimini ta canza-sheka. Blessing Onuh wanda diyar David Mark ce, ta bar APGA, ta koma jam’iyyar APC.

12. Yakubu Abdullahi

PRP ta yi babban rashi a majalisar wakilan. Hon. Yakubu Abdullahi ya sauya-sheka daga jam’iyyar da ba ta shi kujera, ya tafi APC a dalilin rikicin Falalu Bello da Sule Bello.

Kun san cewa Elisha Ishaku Abbo mai wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar dattawa ya sauya-sheka a 2020, ya bar PDP, ya koma APC.

Sanata Elisha Ishaku Abbo ya kuma ce zai nemi takarar gwamnan jihar Adamawa a zaben 2023.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel