2023: Wasu gwamnonin APC huɗu sun matsa wajen zawarcin Jonathan

2023: Wasu gwamnonin APC huɗu sun matsa wajen zawarcin Jonathan

- Har yanzu rade-radin cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, zai koma APC basu daina yawo ba a kafafen yada labarai ba

- Wasu rahotanni sun bayyana cewa gwamnonin APC na son jawo Jonathan zuwa jam'iyyar domin yin takarar shugaban kasa a 2023

Wasu gwamnonin jam'iyyar APC huɗu sun fara yunƙurin janyo tsohon shugaban jam'iyyar APC. Gwamnonin gabaɗayansu daga Arewa suke,kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa a ƙarshen makon.

An rawaito cewa tawagar wasu ƴan siyasa 10 daga kudu,wanda suka haɗa da wani jigon siyasa daga Bayelsa,asalin jihar da tsohon shugaban ƙasar ya fito,sune suka fara yaɗa manufarsu.

Tawagar,wadda wani jagoran jam'iyyar APC daga Bayelsa da wani na hannun damar shugaba Jonathan sun yi zaman ganawa har sau biyu don tattaunawa akan fara yaƙin neman zaɓensa.

Wata majiya mai tushe,wacce ta tabbatar da hakan, ta ce Gwamnonin Arewa suna son gwamnonin Kudu su fara yaƙin neman zaɓe kafin su kuma, daga baya, su marawa tafiyar baya don gamsar da jam'iyyar APC ta bashi tikitin takarar shugaban ƙasa.

KARANTA: Na barku da Allah akan zargin da kuke min; Obasanjo ya waiwayi tarihin marigayi Yar'adua

Majiyar The Nation ta ce an fara wannan tsarin ne da manufar Kudu maso Kudu su ƙarasa wa'adin mulkinsu a shekarar 2023 sannan su fara yaƙin neman zaɓen 2023.

Majiyar tace; "Fitattun ƴan siyasa 10 daga jihar Bayelsa sun zo wuri guda a matsayin tawaga ɗaya. Aikinsu shine fara yaɗa manufa kan buƙatar kudu maso kudu ta ƙarasa wa'adin mulkinta.

2023: Wasu gwamnonin APC huɗu sun matsa wajen zawarcin Jonathan
2023: Wasu gwamnonin APC huɗu sun matsa wajen zawarcin Jonathan
Source: Twitter

"Sun yarda cewa kamar yadda kowanne yanki ya samar da shugaban ƙasar da ya yi mulki tsawon shekara takwas,ya kamata suma a basu damar yin sharafinsu su ƙarasa wa'adinsu.

"Gwamnonin Arewa huɗu da ke goyon bayan Jonathan a 2023 suna son Kudu maso Kudu su fara yaɗa manufarsu tare da yaƙin neman zaɓe,su kuma sai su marawa tafiyar baya.

"Sun fi son ace maganar ta fara fitowa daga yankinta wato Kudu maso Kudu tunda ance waƙa a bakin mai ita ta fi zaƙi."

Majiyar ta ƙara da cewa tuni tawagar ƴan siyasa 10 ta samu ganawa da Tsohon shugaba Jonathan kuma nan ba da jimawa ba zasu tattauna da gwamnonin Arewa da ke cikin tafiyar.

KARANTA: IGP Adamu, DIG 3, da AIG goma zasu yi ritaya a mako guda

Majiyar ta ce,Jonathan ya nuna sha'awarsa ƙarara game da tafiyar wanda hakan ne dalilin da yasa bai fito fili ya ƙaryata raɗe-raɗin cigaba da neman shugabancin ƙasa ba a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.

"Shirin wannan gwamnoni shine Jonathan ya karɓi mulki sannan ya miƙawa Arewa mulki da zarar ya kammala wa'adin shekaru huɗun da suka rage masa.

"Arewar na ganin cewa wa'adinsu ƙarƙashin Marigayi Shugaba Umaru Musa Ƴar'Adua bai ƙare ba amma mutuwa ta yi katsalandan ta gimtse shi kuma suna buƙatar ɗorawa da mulki a babban zaɓen da za'a sake bayan na shekarar 2023," a cewar majiyar.

Majiyar ta ce gawurtattun ƴan siyasa a gwamnatin jihar Bayelsa sun shirya tsaf don goyawa tafiyar baya koda hakan na nufin sauya sheƙarsu zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

"Idan har shirin ya tafi yadda aka tsara,Jonathan zai koma jam'iyyar APC kuma ƴan siyasa da dama daga jam'iyyar PDP zasu biyo bayansa don cigaba da mara masa baya," a cewar majiyar.

Wani aminin tsohon shugaba Jonathan kuma mai hasashe kan al'amuran da suka shafi al'umma,Wisdom Kuti ya ce babu wani abu na ba dai-dai ba a dawo da tsohon Shugaban ƙasa Jonathan zuwa fadar Aso Rock.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel