Gwamnan Zamfara ya yi magana game da rade-radin barin PDP, saboda ya samu tazarce a 2023

Gwamnan Zamfara ya yi magana game da rade-radin barin PDP, saboda ya samu tazarce a 2023

- Muhammad Bello Matawalle ya ce ba harkar siyasa ya sa a gaba yanzu ba

- Dodo ya ce ba ya tsoron su Sanata Kabiru Marafa da Abdulaziz Yari a siyasa

- Gwamnan ya bayyana cewa dai aka buga tamburan siyasa, to zai yi nasara

Gwamna Muhammad Bello Matawalle na Zamfara ya yi watsi da rahotannin da ke cewa zai koma jam’iyyar APC saboda ya samu damar yin tazarce a kan mulki.

Muhammad Bello Matawalle wanda ya zama gwamnan jihar Zamfara a dalilin hukuncin kotu a sakamakon rikicin jam’iyyar APC a 2019, ya ce ya na nan a PDP.

Tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Sani Yariman-Bakura ya yi hira da ‘yan jarida, inda ya shaida cewa su na kokarin jawo gwamnan ya sauya-sheka zuwa APC.

Bello Matawalle ya tabbatar da cewa babu gaskiya a wannan rade-radi, ya ce babban abin da ke gabansa shi ne ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

KU KARANTA: Idan iyayenka sun haifeka 'dan Halas... Matawalle ya kalubalanci Yari

Gwamnan ya ce ba harkar siyasa ya sa gaba a yanzu da ‘yan bindiga su ka addabi jihar Zamafara ba.

“Matsala ta ita ce sha’anin rashin tsaron jihar Zamfara a halin yanzu. Masu wannan kulle-kulle, su na yi ne saboda son kansu, saboda a matsayina na gwamnan da ke fuskantar rikicin ‘ya bindiga da sauran kalubale, bai kamata in biye wa siyasa ba.” Inji Matawalle.

"Gare ni, aiki na shi ne in maida hankali na wajen gudanar da mulki nagari, in kare rayukan al’umma. Ba na kawo batun siyasa a yanzu, rashin tsaro ke gaba na.”

Gwamnan Zamfara ya yi magana game da rade-radin barin PDP, saboda ya samu tazarce a 2023
Gwamna Bello Matawalle Hoto: BBC
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamna Matawalle ya jinjina yiwuwar barin PDP

“Kun san cewa lakabi na shi ne ‘Dodo, kuma sai dai a ji tsoron ‘Dodo’. Ba za su iya gwabzawa da ni ba. kamar yadda na ce wannan harka ce ta siyasa.” a cewarsa.

“Idan lokacin ya zo an buga gangar siyasa, za a ga yadda za ta kare.” Matawalle ya fada wa Daily Trust.

A makon nan mun tattaro maku duka wasu fitattun sauye-sauyen sheka da aka yi daga jam'iyyun adawa zuwa APC mai rinjaye a majalisar tarayya bayan babban zaben 2019.

Yakubu Dogara, Ali Datti Yako, da ‘Diyar David Mark su na cikin wadanda su ka dawo APC.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel