Za muyi amfani da dabaran Katsina wajen ceto yan makarantan Neja, Ministan Tsaro

Za muyi amfani da dabaran Katsina wajen ceto yan makarantan Neja, Ministan Tsaro

- Majalisar wakilai ta karbi bakuncin sabbin hafsoshin tsaron da Buhari ya zaba

- Buhari ya aikesu majalisar don tantancesu da tabbatar da su

- Wannan shine karo na farko da hafsoshin tsaro zasu je majalisa don tantancesu

Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi, ya bayyana cewa hukumar Sojoji za ta yi amfani da dabarar da akayi amfani wajen ceto daliban Kankara domin ceto daliban makarantar gwamnati dake Kagara, a jihar Neja.

Magashi, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a zauren majalisar wakilan tarayya ranar Talata yayinda ake tantance sabbin hafsoshin tsaron da shugaba Buhari ya nada, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ministan ya ce hafsoshin tsaron za su bazama aiki ana kammala tantancesu.

Yace: "Mun nuna bajintarmu wajen dakile irin wannan matsalan. Mun yi a Katsina; lokacin da aka sace yara, muka dawo dasu cikin kwanaki biyu. Muna kyautata zaton cewa yanzu ma haka zamuyi domin dawo da su. Muna shiri."

"Bamu samu bayanan abubuwan dake faruwa a jihar Neja ba har yanzu, amma ina da tabbacin cewa kafin rana ta fadi, zamu samu cikakken labarin halin da ake ciki a jihar Neja."

KU KARANTA: Ya kamata a kafa doka kan man canza launin fata (Bilicin), Tinubu

Za muyi amfani da dabaran Katsina wajen ceto yan makarantan Neja, Ministan Tsaro
Za muyi amfani da dabaran Katsina wajen ceto yan makarantan Neja, Ministan Tsaro
Asali: UGC

DUBA NAN: An kafa kwamiti na musamman don binciken jami'in Hisban da aka kama da matar aure

Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah-wadai da sace dalibai da ma'aikatan makarantar GSSS dake Kagara, jihar Neja a ranar Talata 16 ga watan Fabrairu.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya wallafa jawaban shugaban kasan a shafinsa na Facebook yau Laraba da misalin karfe 11:44 na safe.

Mun kuma ji cewa, babban mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Mohammed Babagana Monguno, Shugaban yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, suna a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Sauran tawagar sune ministan labarai, Lai Mohammed da takwaransa na harkokin yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel