An kafa kwamiti na musamman don binciken jami'in Hisban da aka kama da matar aure

An kafa kwamiti na musamman don binciken jami'in Hisban da aka kama da matar aure

- An damke babban jami'in Hisbah a dakin otal tare da wata mata, yan sanda suka ce

- Hukumar Hisbah ta shahara da kama mutane masu ayyukan alfasha a jihar Kano

- Lokuta da dama, hukumar ta damke karuwai, yan giya da sauran su

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kafa kwamitin mutum biyar domin binciken Sani Remo, daya daga cikin manyan jami'an hukumar Hisbah kan zargin kamashi da matar aure a Otal

TheCable ta ruwaito cewa kakakin hukumar Hisbah, Lawal Fagge, ya bayyana ranar Laraba cewa an baiwa kwamitin kwanaki uku su kammala bincikensu kuma su dawo da bayani.

Fagge ya ce bayan an kammala binciken, hukumar za ta dauki matakin da ya dace kan jami'in.

"Amma idan sakamakon binciken ko shawarin sun fi karfin hukumar, za'a mika lamarin da hukumar da ta dace don daukan mataki," yace.

Yayinda aka tambayesa inda aka ajiye jami'in da ake zargi da laifin, ya ce an sakeshi har zuwa lokacin da aka kammala binciken saboda ba'a tabbatar ya aikata laifin ba.

KU KARANTA: Jerin manyan mutanen da suka shiga jam'iyyar APC cikin mako guda

An kafa kwamiti na musamman don binciken jami'in Hisban da aka kama da matar aure
An kafa kwamiti na musamman don binciken jami'in Hisban da aka kama da matar aure
Asali: UGC

Rahotanni sun ce dan sanda daga ofishin Noman's Land ne ya kama Mista Rimo a dakin wani otel a yankin Sabon Gari da ke Kano.

Majiyoyi daga rundunar yan sanda sun ce sun samu rahotanni ne game da shi sannan suka garzaya suka kama shi tare da matar a dakin.

A baya Mista Rimo shine jami'in tawagar yaki da masu karuwanci na hukumar ta Hisbah wanda karuwai ke shakkarsa sosai a yankin na sabon gari.

A halin yanzu shine jami'in da ke kula da sashin masu hana bara a Kano.

DUBA NAN: Jerin wadanda suka rike mukamin shugaban hukumar EFCC a tarihin Najeriya

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel