Yanzu Yanzu: Sheikh Gumi ya yi alkawarin ziyartan garin Kagara kan sace dalibai da aka yi

Yanzu Yanzu: Sheikh Gumi ya yi alkawarin ziyartan garin Kagara kan sace dalibai da aka yi

- Sheikh Ahmad Gumi ya bayar da tabbacin taimakawa wajen nemo mafita kan sace daliban da aka yi kwanan nan

- Jigon na arewa yayi wannan alkawarin ne a ranar Laraba, 17 ga watan Fabrairu, yayin ziyarar da ya kaiwa gwamna Abubakar Sani Bello

- Gumi ya bayyana sace daliban Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati a jihar Neja a matsayin abin takaici

Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar ya nuna cewa Sheikh Ahmad Gumi ya yi alkawarin ziyartar Kagara, garin Neja, inda aka sace daliban Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara.

Fitaccen malamin addinin Islama ya yi sanarwar ne bayan ya ziyarci gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka Soji 7, sun koresu daga barikinsu a Borno

A cewar Gumi, tattaunawar da aka yi da Bello sun ta'allaka ne kan hanyoyi da dama da za su taimakawa gwamnatin jihar Neja wajen nemo hanyoyin magance rashin tsaro.

Ya ci gaba da bayyana cewa yana kan hanyarsa ta zuwa jihar Kebbi amma ya yanke shawarar tsayawa a Minna, don tattaunawa da gwamnan kan lamarin.

Malamin wanda ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da ya ziyarci jihar Neja ya bayyana satar da aka yi kwanan nan a matsayin abin takaici.

A gefe guda, Bima Enagi, sanata mai wakiltar Neja ta kudu, ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta nuna gazawa wajen magance matsalar rashin tsaro.

Enagi ya fadi hakan ne a zauren majalisar dattijai a ranar Laraba yayin da yake bayar da gudummawarsa ga wata muhawarar kan kudirin da Mohammed Sani Musa, sanata mai wakiltar gabashin Niger ya gabatar.

KU KARANTA KUMA: Mummunar gobara ta barke, gidaje 620 sun kone na 'yan gudun hijira a Maiduguri

Musa ya ja hankalin takwarorinsa a kan sace wasu daliban makarantar sakandare da ke Kagara, dayan bindiga suka yi a jihar Neja.

Mun kuma ji cewa, babban mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Mohammed Babagana Monguno, Shugaban yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, suna a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Sauran tawagar sune ministan labarai, Lai Mohammed da takwaransa na harkokin yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi.

Wannan yana daga cikin kokarin da gwamnatin tarayya ke yin a ceto yaran kwalejin kimiya ta gwamnati, Kagara wanda yan bindiga suka sace a daren jiya Talata, 16 ga watan Fabrairu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel