Buhari ya tura jami'an tsaro jihar Neja don su kwato daliban da aka sace

Buhari ya tura jami'an tsaro jihar Neja don su kwato daliban da aka sace

- Biyo bayan harin da 'yan ta'adda suka kai wata makaranta a Neja, Buhari yayi Allah-wadai

- Shugaban ya nuna rashin jin dadinsa tare da tura sojoji nan take zuwa jihar don ceto yaran

- Shugaban ya kuma tura wasu masu ruwa da tsaki a gwamnati don shawo kan matsalar

Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah-wadai da sace dalibai da ma'aikatan makarantar GSSS dake Kagara, jihar Neja a ranar Talata 16 ga watan Fabrairu.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya wallafa jawaban shugaban kasan a shafinsa na Facebook yau Laraba da misalin karfe 11:44 na safe.

A cewar shugaban, ya samu labarin faruwar lamarin kai harin 'yan ta'adda da ya auku cikin dare, wanda har ya zuwa yanzu ba a gano adadin ma'aikata da daliban da aka sace ba.

KU KARANTA: Idan Fani Kayode ya koma APC, to PDP ce zata ruguje ba shi ba, in ji jigon PDP

Buhari yayi Allah-wadai da sace daliban Neja, ya kuma tura jami'an tsaro jihar
Buhari yayi Allah-wadai da sace daliban Neja, ya kuma tura jami'an tsaro jihar Hoto: Punch News
Asali: UGC

Shugaban ya kuma kara da cewa ya tura jami'an 'yan sanda da sojoji don tabbatar da an ceto wadanda aka sacen.

Hakazalika ya tura wasu daga cikin tawagar ministocinsa zuwa jihar ta Neja don tabbatar da cewa an ceto wadanda aka sacen, tare da ganewa da jami'an jihar, shugabannin al'umma, iyayen yaran da abin ya shafa da kuma iyalan ma'aikatan makarantar.

Shugaban yace: "Ina jajantawa iyalai da iyayen wadanda lamarin a faru dasu.

"Na bada umarnin tura sojoji da 'yan sanda don ceto daliban da ma'aikatan makarantar da aka sace." ya kara da cewa.

A ci gaba da jawabinsa, shugaba Muhammadu Buhari ya tausasa zukatan iyalan wadanda aka sacen da cewa, "Addu'o'inmu suna tare da dangin wadanda harin ya rutsa da su." in ji shi

A karshe ya tabbatar cewa gwamnatinsa za ta dauki mataki akan lamarin, sannan zata ci gaba da kokari don gwagwarmayar yaki da 'yan ta'adda.

KU KARANTA: An kashe mana mutane sama da 23 a rikicin Ogun, in ji Sarkin Fulani

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ayyukan soji da ke gudana a yankin Arewa maso Gabas za su dore domin tabbatar da tsaron yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Babagana Zulum ya nakalto shugaban yana fadar haka ne bayan wata ganawar sirri da yayi da wata tawaga daga jihohin Borno da Yobe.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.