Ya kamata a kafa doka kan man canza launin fata (Bilicin), Tinubu

Ya kamata a kafa doka kan man canza launin fata (Bilicin), Tinubu

- Kowa ya zama mai sana'an kayan shafe-shafe yanzu, cewar Sanata Tinubu

- Sanatar ta bukaci hukumar NAFDAC ta dau mataki kan masu hada man bilicin

Sanata Remi Tinubu ya bukaci majalisar dattawan tarayya ta samar da doka kan sayar da kayan shafe-shafe, musamman man sauya launin jiki watau man Bilicin.

Uwargidar jigon APC ta gabatar da kudirinta yayin zaman majalisa a ranar Talata, 16 ga Febrairu, 2021, Vanguard ta ruwaito.

Ta bukaci hukumar NAFDAC da ta tashi tsaye domin kare yan Najeriya daga kayan shafe-shafen da ka iya cutar da su.

Remi Tinubu ta bayyana damuwarta kan yadda kananan yan kasuwa ke hada kayan shafe-shafe iri-iri ba tara da sa hannun gwamnati ba.

A cewarta, wadannan kayan sun cika kasuwannin Najeriya.

Tace: "Majalisar dattawa na nuna damuwarta saboda da matukar wahala a tabattar da inganci, tsafta, da bin ka'idoji lokacin da aka hada wadannan kayayyaki."

DUBA NAN: Jerin wadanda suka rike mukamin shugaban hukumar EFCC a tarihin Najeriya

Ya kamata a kafa doka kan man canza launin fata (Bilicin), Tinubu
Ya kamata a kafa doka kan man canza launin fata (Bilicin), Tinubu Credit: @NGRSenate
Asali: UGC

DUNA NAN: Jerin manyan mutanen da suka shiga jam'iyyar APC cikin mako guda

A wani labarin kuwa, a ranar Talata ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da bayar da kwangilar Naira miliyan 83.4 don rigakafin dabbobi, The Nation ta ruwaito.

Yarjejeniyar ta hada da samar da kwalabe 8,250 na maganin rigakafin Bovine Pleuropneumonia (CBPP) da kuma kwalabe 20,000 na maganin rigakafin Peste des Petits Ruminants (PPR).

Shirin allurar rigakafin a duk fadin jihar, wanda zai fara nan da wasu makonni zai dauki shanu 800,000 da kuma kananan dabbobi miliyan 1 a kowace shekara.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel