Fusatattun dandazon mutane sun lalata gidan mataimakin gwamnan jihar Niger

Fusatattun dandazon mutane sun lalata gidan mataimakin gwamnan jihar Niger

- 'Yan kasuwa da fusatattun matasa sun yi barna a gidan mataimakin gwamnan jihar Niger

- Dandazon mutanen da yan kasuwan sun harzuka ne bayan jami'an hukumar cigaban birane ta rusa wasu shaguna a kasuwa

- - Shugaban riko na hukumar cigaban birane na Niger, a bangarensa ya ce an dade sa gargadin masu shagunan kan cewa su tashi don ba bisa ka'ida aka yi ginin ba

Mazauna layin Brighter a garin Minna a jihar Niger sun shiga rudani a safiyar ranar Talata a yayin da fusatattun matasa da masu shaguna a wata karamar kasuwa da ke unguwar suka lalata gidan mataimakin gwamna da ke Minna a jihar Niger.

A cewar majiya, lamarin ya faru ne misalin karfe 11 na safe a yayin da matasa da yan kasuwa da aka rusa musu shaguna suka huce fushinsu a gidan mataimakin gwamnan.

Wata majiya da ta nemi a boye sunan ta ta shaidawa The Punch cewa yan kasuwar sunyi ikirarin ba a bamu umurnin su tashi ba kawai sai suka ga motocin rushe gine-gine suna rusa shaguna ba tare da an bari mutane sun kwashe dukiyoyinsu da sauran kaya masu muhimmanci ba.

DUBA WANNAN: An fara bincikar jami'in Hisbah da aka kama da matar aure a ɗakin Otel a Kano

Fusatattun dandazon mutane sun lalata gidan mataimakin gwamnatin jihar Niger
Fusatattun dandazon mutane sun lalata gidan mataimakin gwamnatin jihar Niger. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Majyar ta ce yan kasuwan sun nemi a yi adalci a rushe gidan mataimakin gwamnan duba da cewa gidan yana wuri daya da shagunan suke.

Majiyar ta ce yan kasuwar sun yi asarar miliyoyin naira sakamakon rushe shagunansu duba da cewa ba a basu damar kwashe kayansu ba.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai hari GSC Kagara a Niger, sun kashe dalibi daya sun sace wasu

Daya daga cikin masu shagunan, Mallam Muritala ya koka kan yadda gwamnatin jihar ta rusa masa shago ba tare da an sanar da shi cewa ya tashi daga shagon ba.

Ya ce, "Ina zaune a shago na kawai suka ce min in fito - da motarsu a gaban shagon - nan take suka fito da ni. Sun rusa shago na baki daya ba tare da sun bari na kwashe kudi na, kaya da wasu abubuwa masu muhimmanci ba. Sun mayar da ni farko. Ba ni da komi yanzu."

A bangarensa, shugaban riko na hukuma cigaban birane na jihar yace zargin ba gaskiya bane, ya kara da cewa an bawa dukkan wadanda suka yi gini a wuraren da ba su dace ba notis na cewa za a rushe.

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel