An fara bincikar jami'in Hisbah da aka kama da matar aure a ɗakin Otel a Kano

An fara bincikar jami'in Hisbah da aka kama da matar aure a ɗakin Otel a Kano

- Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kafa kwamiti na bincike kan wani jami'in ta da ake zargi da kwartanci da matar aure

- Jami'an yan sanda ne suka kama jami'in Hisban a wani dakin Otel tare da wata matar aure a yankin Sabon Gari na Kano

- Hukumar ta ce ta bawa kwamitin kwanaki uku ya kammala bincikensa kuma za a hukunta jami'in idan an tabbatar ya aikata laifin

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kafa kwamiti mai mutum biyar domin fara bincike kan jami'inta, Sani Rimo, wanda aka ce an kama shi da matar aure a cikin dakin Otel a Kano.

Babban Kwamandan Hisbah, Harun Ibn-Sina, ya tabbatar da cewa an bawa kwamitin wa'adin kwanaki uku ta yi bincike kan lamarin, Daily Nigerian ta ruwaito.

An fara bincikar jami'in Hisbah da aka kama da matar aure a ɗakin Otel a Kano
An fara bincikar jami'in Hisbah da aka kama da matar aure a ɗakin Otel a Kano. Hoto: @daily_nigerian
Asali: UGC

"Na kafa kwamitin bincike na kuma na bata wa'adin kwanaki 3 domin ta bata rahoton ta. Na kuma gayyaci bangarorin da abin ya shafa domin su bada ba'asi.

"Hisbah tana da dokokin ta, kuma idan muka same shi da laifi, za mu dauki matakin da ya dace a kansa bisa yadda dakokin mu suka tanada," in ji shi.

KU KARANTA: Umar Faruk: Matashin da aka yanke wa hukunci saboda ɓatanci a Kano ya bar Nigeria

Rahotanni sun ce dan sanda daga ofishin Noman's Land ne ya kama Mista Rimo a dakin wani otel a yankin Sabon Gari da ke Kano.

Majiyoyi daga rundunar yan sanda sun ce sun samu rahotanni ne game da shi sannan suka garzaya suka kama shi tare da matar a dakin.

A baya Mista Rimo shine jami'in tawagar yaki da masu karuwanci na hukumar ta Hisbah wanda karuwai ke shakkarsa sosai a yankin na sabon gari.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaban kamfen ɗin Atiku, Gbenga Daniel, ya fice daga PDP ya koma APC

A halin yanzu shine jami'in da ke kula da sashin masu hana bara a Kano.

Kawo yanzu yan sanda ba su yi martani kan lamarin ba.

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: