Yanzu-yanzu: Bidiyon hatsarin jirgin ƙasa da trela a Legas

Yanzu-yanzu: Bidiyon hatsarin jirgin ƙasa da trela a Legas

- Jirgin kasa ya yi hatsari da babban mota wacce da dauke da abincin dabobi a Iju-Ishaga a Legas

- Hatsarin ya faru ne misalin karfe 8.52 na safiyar ranar Litinin 15 ga watan Fabrairun shekarar 2020

- Shaidun gani da ido sun kuma ce babbar motar ta bige wani mai adaidaita sahu amma ya tsira da ransa

Jirgin kasa ya yi da karo da babban mota (trela) makare da abincin dabobi a Iju-Ishaga, layin Jonathan Coker a karamar hukumar Ifako-Ijaiye da ke jihar Legas, The Cable ta ruwaito.

Shaidun ganin ido sun shaidawa majiyar Legit.ng cewa babbar motar ta kuma murkushe wata a dai-daita sahu.

DUBA WANNAN: Babu wanda ya isa ya kore mu daga yankin kudu maso yamma, in ji Miyetti Allah

Bidiyon hatsarin jirgin kasa da babban mota a Legas
Bidiyon hatsarin jirgin kasa da babban mota a Legas. Hoto: @thecableng
Source: Twitter

Jami'an tsaro a halin yanzu suna can suna kokarin ganin al'amurra sun daidaita a wurin da hatsarin ya faru misalin karfe 8.52 na safiyar yau.

Hatsarin ya janyo cinkoson ababen hawa a yankin hakan yasa ake bawa masu ababen hawa shawarar sun sauya hanya.

A lokacin da ake hada wannan rahoton, babu wanda ya rasa ransa sakamakon hatsarin.

Dreban a dai-daita sahun ya tsira da ransa.

KU KARANTA: Turkmenistan: Shugaban ƙasa ya naɗa ɗansa a matsayin 'mataimakinsa'

Ga bidiyon a kasa:

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel