Sarkin Zazzau ya naɗa Abdulrahman Nuhu Bayero a matsayin sabon Ɗan Iyan Zazzau

Sarkin Zazzau ya naɗa Abdulrahman Nuhu Bayero a matsayin sabon Ɗan Iyan Zazzau

- Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamall ya naɗa Abdulrahman Nuhu Bayero sarautar Ɗan Iyan Zazzau

- Sanarwar tana dauke ne cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun sakataren masarautar Alhaji Barau Aliyu Musa

- Abdulrahman Nuhu Bayero, ma'aikacin Radio Nigeria Kaduna ɗa ne ga tsohon Dan Iyan Zazzau, Alhaji Nuhu Bayero

Sarkin Zazzau a jihar Kaduna, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya naɗa Abdulrahman Nuhu Bayero a matsayin sabon Ɗan Iyan Zazzau.

A wasika mai ɗauke da sa hannun sakataren masarautar kuma Sarkin Fulanin Zazzau, Alhaji Barau Musa Aliyu ta ce kwamitin naɗi za ta sanar da ranar da za a yi nadin sarautar a fadar Sarkin Zazzau.

Sarkin Zazzau ya naɗa Abdulrahman Nuhu Bayero a matsayin sabon Iyan Zazzau
Sarkin Zazzau ya naɗa Abdulrahman Nuhu Bayero a matsayin sabon Iyan Zazzau. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rashin tsaro: An maka Buhari da Makinde a kotu kan rikicin makiyaya a Oyo

Masarautar ta Zazzau ta taya Abdulrahman Nuhu Bayero murna bisa naɗin tare da addu'ar Allah ya bashi basira, tsawon rai ya kuma masa jagoranci a rayuwa.

Sabon ɗan Iyan Zazzau din da aka naɗa ma'aikacin sashin labarai da al'amuran yau da kullum ne a Radio Nigeria Kaduna.

Ya yi aiki a matsayin edita a tashan hukumar da ke Kaduna, mai aikewa da rahotanni a Zaria, shugaban sashin labarai, Radio Nigeria FM a Dutse, Jihar Jigawa.

KU KARANTA: Bidiyon rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan

Sabon wanda aka yi wa naɗin ɗan Marigayi Iyan Zazzau Nuhu Bayero ne.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Source: Legit.ng

Online view pixel