Rashin tsaro: An maka Buhari da Makinde a kotu kan rikicin makiyaya a Oyo

Rashin tsaro: An maka Buhari da Makinde a kotu kan rikicin makiyaya a Oyo

- An yi karar Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan Oyo, Seyi Makinde kan batun rashin tsaro a Oyo

- Karar da aka shigar a madadin Falana Chambers na son kotu ta umurci wanda ake karar su kama tare da bincikar duk wani makiyayi da ake zargi da laifi a Oyo

- Har wa yau, takardar kara na neman a umurci wanda ake karar su tabbatar sun kare rayyuka da dukiyoyin mutanen Oyo

Femi Aborisade, wani lauya ya yi karar Shugaba Muhammadu Buhari da Seyi Makinde, gwamnan Oyo a kotu kan zargin kashe-kashe da garkuwa da ake yi a karamar hukumar Ibarapa ta jihar, The Cable ta ruwaito.

Rikici ya barke a Ibarapa makonni biyu da suka shude bayan wa'addin mako daya da Sunday Adeyemo (Igboho) ya bawa makiyaya su bar garin.

Rashin tsaro: An maka Buhari da Makinde a kotu kan makiyaya a Oyo
Rashin tsaro: An maka Buhari da Makinde a kotu kan makiyaya a Oyo. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Jiragen yakin NAF sun sake halaka yan bindiga masu yawa a Kaduna

Igboho ya zargi makiyaya da kashe-kashe da garkuwa da mutane da ake yi a garin.

An shigar da karar mai lamba FHC/IB/CS/17/2, a ranar Laraba a madadin mai shigar da karar, Falana dan Falana Chambers a kotun tarayya da ke Ibadan.

Atoni janar na kasa, Abubakar Malami, Ngozi Onadeko, kwamishinan yan sandan Oyo suma suna cikin wadanda aka lissafa a karar.

Mai shigar da karar na son kotu ta umurci wadanda ake kararsu da su "kama tare da bincikar duk wani makiyayi da ake zargi da fashi, garkuwa, kisa, kutse, da sauran laifuka a garuruwan Ibarapa central, Ibarapa east, Ibarapa north, har da Igangan, Atisbo, Irepo, Iseyin, Itesiwaju, Iwajowa, Kajola, Oorelope, Olorunsogo, da kananan hukumomin Saki East da West."

KU KARANTA: Tsohon gwamnan Zamfara, Yerima, ya gurfana gaban kwamiti kan zargin 'azabtar da ɗan kasuwa'

Har wa yau, takardar karar tana neman a umurci wadanda ake kara su dauki matakan da suka dace don kare rayyuka da dukiyoyin dukkan mutanen yankin.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya tuntuɓarsa kai tsaye a shafinsa na Twitter @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel