Bidiyon rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan

Bidiyon rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan

- Mutum daya ya rasu sakamakon rikicin da ta barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan

- An kuma kone wasu gidaje da lalata dukiyoyi masu yawa sakamakon rikicin da ya faru a Sasa

- An yi kokarin ji ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar da na Amotekun amma ba a same su ba

Mutum daya ya riga mu gidan gaskiya a ranar Juma'a sakamakon rikici da ta barke tsakanin Yarbawa da Hausawa mazauna garin Sasa da ke Ibadan a jihar Oyo.

An kuma kone gidaje tare da bannata dukiyoyi a rikicin da kawo yanzu ba a tabbatar da abinda ya yi sanadinsa ba, The Cable ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Rashin tsaro: An maka Buhari da Makinde a kotu kan rikicin makiyaya a Oyo

Bidiyon rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan
Bidiyon rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Yan kasuwa a kasuwar Sasa, da ake sayar da tumatur da sauran kayan miya ba su samu idon sayar da kaya a yau ba saboda barkewar rikicin.

Jami'an yan sanda da na Amoketun sun isa wurin domin tabbatar da zaman lafiya.

An yi kokarin ji ta bakin kakakin yan sandan jihar Olugbenga Fadeyi domin jin ta bakinsa amma hakan bai yi wu ba domin bai amsa wayarsa ba.

Kazalika, Olayinka Olayanju, kwamandan Amotekun na jihar shima bai amsa sakon tes da aka aike masa ba.

KU KARANTA: Ana iya amfani da NIN don gano ɓata-garin makiyaya, in ji Ganduje

Ga bidyon rikicin a kasa:

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: