‘Ya ‘yan jam’iyya sun tarwatse bayan tagwayen bama-bamai sun tashi a ofishin PDP

‘Ya ‘yan jam’iyya sun tarwatse bayan tagwayen bama-bamai sun tashi a ofishin PDP

- Wasu abubuwa sun yi bindiga a sakatariyar jam’iyyar PDP a garin Fatakwal

- Mutane da dama duk sun tsere sun bar sakatariyar domin su tsira da ransu

- An ji wannan abin ne a lokacin da ake fitar da ‘yan takara na zaben Kansiloli

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an ji wasu kara daga wurare biyu a babbar sakatariyar jam’iyyar PDP a garin Fatakwal, jihar Ribas.

Ana zargin cewa bama-bamai ne su ka tashi a ofishin na PDP. Wannan abu ya faru ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Fubrairu, 2021.

Majiyar ta bayyana cewa wannan abu kamar bam, ya tashi ne daga cikin wata mota kirar SUV, da aka ajiye a gaban sakatariyar ta PDP.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an ji wannan kara ne da kimanin karfe 3:00 na yamma, wanda ya tsorata wadanda ke 'yan ofishin da kewaye.

KU KARANTA: Ana zargin ‘Yan Shi’a da neman jawo husuma a Abuja

Lamarin ya auku ne a daidai lokacin da ake kokarin tantance ‘yan takarar fitar da gwani na jam’iyyar PDP a zaben Kansiloli da za ayi a Ribas.

Hakan ya sa ‘ya ‘yan jam’iyyar duk su ka tsere domin su tsira da rayuwarsu, daga cikin karar.

Kawo yanzu babu wani mutum ko kungiya da ta yi ikirarin yin wannan aiki. Daga baya dukmutanen da su ka tsere sun dawo ofisoshinsu.

Mai magana da yawun bakin PDP a jihar Ribas, Tambari Sydney Gbara, ya ki yi wa ‘yan jarida bayani game da wannan abin da ya auku a jiya.

KU KARANTA: Rajistar APC da ake yi ya saba doka, na yi ne kawai dai... - Oshiomhole

‘Ya ‘yan jam’iyya sun tarwatse bayan tagwayen bama-bamai sun tashi a ofishin PDP
Gwamnan Jihar Ribas Hoto: Ezenwo Nyesom Wike
Asali: Facebook

Wasu na zargin cewa zargin da ake yin a kakaba ‘yan takara ta karfi da yaji a zaben kananan hukumoin ne ya jawo wasu su ka yi wannan danyen aiki.

A yau ne ku ka ji cewa an tsige shugaban karamar hukumar Emohua, jihar Ribas. High Chief Tom Aliezi zai bar mukamin da yake kai bayan samunsa da laifi.

An cin ma wannan matsayar ne bayan shugabannin kwamitin wucin gadi sun yi taro a kansa.

An yi nasarar cire Tom Aliezi ne yayin zaman majalisar gudanarwa bayan samun rinjaye na kashi biyu cikin uku na mambobin majalisar ta Emohua.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki.

Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai (Info Mgt), kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel