Yanzu-yanzu: An tsige shugaban karamar hukumar PDP

Yanzu-yanzu: An tsige shugaban karamar hukumar PDP

- An tsige mai girma shugaban karamar hukumar Emohua a jihar Rivers High Chief Tom Aliezi

- An tsige Tom Aliezi ne bayan mataimakin shugaban majalisar ya gabatar da kudirin

- Ana zargin shi da bannatar da kudade, gaza shayar da mutanensa romon domokradiya da saba wasu dokoki

An tsige shugaban karamar hukumar Emohua a jihar River mai suna High Chief Tom Aliezi daga mukaminsa.

An yi nasarar cire shi yayin zaman majlisar bayan samun rinjaye na kashi biyu cikin uku na mambobin majalisar Emohua a ranar Alhamis 11 ga watan Fabrairu kamar yadda The Nation ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan Zamfara, Yerima, ya gurfana gaban kwamiti kan zargin 'azabtar da ɗan kasuwa'

Yanzu-yanzu: An tsige shugaban karamar hukumar PDP
Yanzu-yanzu: An tsige shugaban karamar hukumar PDP. Hoto: @AgumaAguma2 @OdumBlessy
Asali: Twitter

Tsige Aliezi ya biyo bayan kudirin da mataimakin shugaban majalisar, Benerd Odike mai wakiltar mazabar Ogbakiri Ward Two ya gabatar a gaban majalisa.

KU KARANTA: Rashin tsaro: An maka Buhari da Makinde a kotu kan rikicin makiyaya a Oyo

Cire shi ya tabbata ne bayan 10 cikin yan majalisa 14 sun jefa kuri'un amincewa da kudirin kan zarginsa da bannatar da kudade, gaza shayar da mutanensa romon domokradiya da saba wasu dokoki.

Chekwas Evans-Woleru, jagorar majalisar, ya ce yan majalisar sun yanke shawarar su tsige Aliezi ne bayan ya gaza bayyana da kansa domin ya kare kansa ko kuma a rubuce game da zargin da ake masa.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164