‘Yan Sanda sun yi ram da wasu daga cikin Mabiyan Sheikh El-Zakzaky za su yi ta'adi a Abuja
- Wasu Mabiya kungiyar IMN sun fada hannun ‘Yan Sandan Najeriya
- Dakarun ‘Yan Sanda sun ce wadannan mutane sun yi niyyar yin ta’adi
- A halin yanzu akwai Mabiya IMN 11 a ragar ‘Yan Sanda a garin Abuja
Rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke birnin tarayya Abuja ta kama wasu mutane biyar daga cikin ‘ya 'yan kungiyar Islamic Movement in Nigeria ta 'yan Shi’a.
Jaridar Punch ta rahoto cewa ‘yan sandan su na tuhumar wadannan mabiya addinin shi’a da laifin yunkurin kai wa al’umma hari, da yi wa dukiyarsu barna.
Mai magana a madadin dakarun ‘yan sanda na birnin tarayya Abuja, ASP Mariam Yusuf ce ta bayyana wannan a ranar Laraba, 10 ga watan Fubrairu, 2021.
ASP Mariam Yusuf ta ce an kama wadannan mutane su na dauke da manyan duwatsu, wanda ake zargin sun yi niyyar amfani da su wajen yi wa jama’a ta’adi.
KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya ce a zauna a sasanta da ‘Yan bindiga
A makon da ya gabata, ‘yan sandan Najeriyar sun yi ram da wasu mabiya kungiyar IMN shida.
Kamar yadda jami’ar ta yi bayani, a halin yanzu mabiyan wannan kungiya ta Islamic Movement in Nigeria 11 ne su ke tsare a hannun jami’an ‘yan sandan kasar.
“An kama mabiyan wannan haramtaciyyar kungiya dauke da manya-manyan duwatsu, wanda su ka yi nufin amfani da su wajen kawo rudani.” Inji ASP Yusuf.
“Bayan haka, da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da mutanen da aka kama a gaban kotu.”
KU KARANTA: An ba maza shawarar auren mata da yawa domin su daina biye-biye
Rundunar ‘yan sanda ta yi kira ga mazauna garin Abuja su cigaba da bin doka, su kwantar da hankalinsu domin ‘yan sanda su na cigaba da kokarin tsare al’umma.
Ku na sane cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta shiga kotu da shugaban kungiyar IMN, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, inda ta ke tuhumarsa da laifuffuka fiye da takwas.
A makonnin da su ka gabata, Ibrahim El-Zakzaky da matarsa, Zeenat El-Zakzaky duk ba su halarci zaman kotun da aka yi, ana sauraron karar da gwamnati ta kai su ba.
Lauyan gwamnati ya gabatar da shaidu daga cikin dakarun sojoji wadanda su ka yi magana a boye.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai (Info Mgt), kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. A bibiye shi a Twitter @mmalumfashi
Asali: Legit.ng