Oshiomhole ya soki aikin da shugaban APC ya kirkiro, ya goyi bayan Tinubu, Akande

Oshiomhole ya soki aikin da shugaban APC ya kirkiro, ya goyi bayan Tinubu, Akande

- Adams Oshiomhole ya na cikin masu adawa da sabunta rajistar jam’iyyar APC

- Tsohon shugaban jam’iyyar ta APC ya ce wannan aikin ya ci karo da dokokinsu

- Oshiomhole ya ce ya sake rajistar ne domin kurum a samu zaman lafiya a APC

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya ce sabunta rajistar da ake yi a APC, ya ci karo da abin da doka da tsarin jam’iyya ta ce.

The Cable ta ce Adams Oshiomhole yayi wannan bayani ne a ranar Talata, a gaban ‘yan jarida bayan ya sabunta rajistarsa a mazabarsa a jihar Edo.

Tsohon gwamnan na jihar Edo ya bayyana cewa APC ta na tafiya ne a kan doka da tsarin mulki, kuma babu inda dokar jam’iyyar ta ce a sake rajista.

“Doka ta ke tafiyar da tsarin APC ba wani mutum ba. Abin da doka ta ce shi ne ayi rajista kurum, kuma na yi rajista a 2014 a karkashin Bisi Akande.”

KU KARANTA: APC za ta birne rikice-rikicen da ya jawo mata matsala a zaben 2019

“Babu inda a doka aka ce sai ‘dan APC ya sabunta ko tabbatar da rajistarsa. Da zarar kayi rajista lokacin da ka shiga, kuma ba ka sauya-sheka ba, shikenan.”

Adams Oshiomhole ya ce: “Saboda haka sabunta rajista, bakon abu ne a cikin dokar jam’iyyarmu.”

“Na yi wannan ne kurum saboda ina son a zauna lafiya, amma wajen yin hakan, dole mu yi hattara ka da mu keta dokoki da tsarin jam’iyya.” Inji Oshiomhole.

Ya ce: “Idan ka ce ni wanda ina cikin wadanda aka kafa APC da su in sake rajista, bayan na yi a baya, kuma ban sauya-sheka ba, na yi rajista sau biyu kenan.”

KU KARANTA: Rajista: Tsohon shugaban jam'iyyar APC ya na tare da Mala Buni

Oshiomhole ya soki aikin da shugaban APC ya kirkiro, ya goyi bayan Tinubu, Akande
Kwamred Adams Oshiomhole Hoto: punchng.com
Asali: UGC

“Da ba mu da rajista, ta ina za mu yi zaben fito da ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2015, inda ‘ya ‘yan jam’iyya mutum miliyan 16 su ka zabi Buhari?”

Tsohon shugaban APC ya ce kamata ya yi a kira aikin da tasa wa, amma ba sake yin rajista ba.

A jiya ne ku ka ji cewa sabon rikici ya tunkaro jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a sakamakon wasu kalamai da aka ji sun fito daga bakin Bola Ahmed Tinubu.

Bola Tinubu wanda ake kyautata zaton zai nemi tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya ce aikin sabunta rijistar 'yan jam'iyyar da ake yi bai da amfani.

Wannan shi ne ra'ayin na-hannun daman Bola Tinubu, shugaban jam'iyyar APC na kasa na farko, Olabisi Akande, akasin tunanin magajinsa, Cif John Oyegun.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel