Gwamna Wike ya ce hukumar NDDC ta 'damfari' jiharsa

Gwamna Wike ya ce hukumar NDDC ta 'damfari' jiharsa

- Barrister Nyesome Ezenwo Wike, gwamnan jihar Rivers da ke yankin Niger Delta ya zargi hukumar NDDC da damfarar jiharsa

- Gwamnan na Rivers ya ce akwai wani yarjejeniyar gina asibiti na hadin gwiwa tsakanin jiharsa da NDDC amma daga baya NDDC ta karbe kudi daga jiharsa ta cinye

- Gwamna Wike ya kuma yi zargin cewa hukumar bata aiki tare da gwamnonin yankin Niger Delta

Gwamnan jihar Rivers Nyesome Ezenwo Wike ya zargi Hukumar Cigaban Yankin Niger Delta, NDDC, da damfarar jiharsa, Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke magana yayin da yan kwamitin majalisar wakilai na NDDC karkashin shugabanta, Olubunmi Tunji-Ojo suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati a Port Harcourt, a ranar Alhamis, gwamnan ya zargi hukumar da rashawa.

Gwamna Wike ya ce hukumar NDDC ta 'damfari' jiharsa
Gwamna Wike ya ce hukumar NDDC ta 'damfari' jiharsa. Hoto: Premium Times
Source: Facebook

Ya ce NDDC sun taba amincewa za su yi hadin gwiwa kan wani aiki na musamman amma daga bisani hukumar ta yaudari gwamnatin jihar.

DUBA WANNAN: Jiragen yakin NAF sun sake halaka yan bindiga masu yawa a Kaduna

"NDDC ta yaudare mu kan ginin Mother and Child Hospital. Sun damfare mu. Sun cimma yarjejeniya da gwamnatin jihar cewa za su gina asibitin yankin mai suna Mother and Child hospital.

"Sun yarda cewa za a kashe N1.7 biliyan kuma gwamnatin jihar za ta bada N800 miliyan su kuma su kawo N900 miliyan. Gwamnatin jihar a lokacin ta biya N800 miliyan sai NDDC ta yi amfani da N400 miliyan cikin kudin ta fara biyan yan kwangila sannan ta yi watsi da yan kwangilar daga karshe yan kwangilar suka tafi. Da muka zo, mun ce mun fasa aikin, ku bamu kudinmu N400 miliyan, abin ya zama matsala. Siyasa ya shigo batun," in ji shi.

Ya ce hukumar bata bibiyar gwamnonin jihohin da ke samar da man fetur.

KU KARANTA: Tsohon gwamnan Zamfara, Yerima, ya gurfana gaban kwamiti kan zargin 'azabtar da ɗan kasuwa'

Wike ya yi kira ga majalisa ta kara jajircewa kan aikinta na sa ido ta ga cewa NDDC ta dena 'karkatar da kudaden da ya dace a yi wa yankin aiki'.

Jagorar tawagar kuma shugaban kwamitin, Tunji-Ojo ya ce sun kai ziyarar ne domin Wike babban mai ruwa da tsaki ne a harkokin NDDC. Ya ce kwamitin za ta tabbata NDDC ta yi aiki da masu ruwa da tsaki na yankin.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

https://hausa.legit.ng/1402247-an-rufe-majalisar-ghana-bayan-mambobi-da-maaikata-168-sun-harbu-da-korona.html

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya tuntuɓarsa kai tsaye a shafinsa na Twitter @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel