Tsohon gwamnan Zamfara, Yerima, ya gurfana gaban kwamiti kan zargin 'azabtar da ɗan kasuwa'

Tsohon gwamnan Zamfara, Yerima, ya gurfana gaban kwamiti kan zargin 'azabtar da ɗan kasuwa'

- Tsohon gwamnan Zamafara, Sanata Ahmed Yerima ya bayyana gaban wata kwamitin shari'a da aka kafa a Abuja

- Wani dan kasuwa ne ya yi karar Yerima kan zargin cin zalinsa ta hanyar amfani da jami'an yan sandan Kaduna da Kano

- Bayan amsa gayyatar, wanda ya yi korafin ya nemi a biya shi diyyar N100m kuma bangarorin biyu sun amince su yi sulhu

Ahmad Yerima, tsohon gwamnan Zamfara ya gurfana wata kwamitin karban korafi da ke zamanta a Abuja kan zarginsa da hannu wurin barazana ga rayuwar wani Musa Wapa, dan kasuwa, The Cable ta ruwaito.

Kwamitin aka kafa don binciken cin zarafin da ake zargin tsohuwar sashin yan sandan SARS da aka ruse ta gayyaci Yerima a ranar 2 ga watan Disamban 2020 bayan Wapa ya shigar da kara.

Tsohon gwamnan Zamfara, Yerima, ya gurfanar gaban kwamitin shari'a kan 'azabtar da dan kasuwa'
Tsohon gwamnan Zamfara, Yerima, ya gurfanar gaban kwamitin shari'a kan 'azabtar da dan kasuwa'. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan tawayen Houthi sun kai hari sun ƙona jirgin saman kasar Saudiyya

Wapa na zargin Yerima da cinna masa yan sandan tawagar IRT inda suka tsare shi na kwanaki shida suna gana masa azaba.

Dan kasuwar, yayin gabatar da hujojinsa a Disamba, ya ce yana bin tsohon gwamnan bashin Naira miliyan 25 saboda siyar masa da tirelolin masara uku daga gonarsa, Rufai Poultry (Nig) Ltd.

Ya kuma bayyana cewa Yerima na binsa bashin Naira miliyan 23.

Sai dai ya ce lokacin da suka yi alkawarin ya biya Yerima bashin Naira miliyan 23 bai cika ba a ranar 30 ga watan Yunin 2020, amma tsohon gwamnan ya biya yan sandan Kano da na IRT a Kaduna kudi suka tsare shi na kwanaki shida suna azabtar da shi.

KU KARANTA: Damfarar N500,000: An yanke wa ma'aikacin gwamnatin Kano shekaru 5 a gidan ɗan kande

Wapa ya bukaci kotun ta umurci tsohon gwamnan ya biya shi diyar Naira miliyan 100.

Da aka fara sauraron korafin a ranar Laraba, Garba Tetengi, wanda ya wakilci Suleiman Galadima, shugaban kotun na musamman, ya tambayi bangarorin biyu idan suna son a basu dama su daidaita kansu.

Bangarorin biyu sun yarda za su sasanta kansu.

Daga bisani, an umurci lauyan kwamitin ya tabbatar bangarorin biyu sun sasanta cikin aminci.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164