Jiragen yakin NAF sun sake halaka yan bindiga masu yawa a Kaduna

Jiragen yakin NAF sun sake halaka yan bindiga masu yawa a Kaduna

- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a Kaduna, Samuel Aruwan ya ce jiragen yakin NAF sun sake kai wa yan bindiga hari

- Wuraren da jiragen suka kai sumame sune da Rahama, Tami, Sabon-Birni, Galadimawa da Ungwan-Farinbatu

- Saura sun hada da Sabuwa, Kutemeshi, Gajere, Sabon Kuyello, Dogon Dawa, Ngade Allah, Kidandan a kananan hukumomin Birnin-Gwari da Giwa

Jiragen Dakarun Sojojin Saman Nigeria, NAF, a ranar Laraba sun halaka yan bindiga masu yawa a mabuyarsu da ke dazukan jihar Kaduna, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida, Mista Samuel Aruwan, ya lissafa wurarren da jiragen suka kai hari inda suka hada da Rahama, Tami, Sabon-Birni, Galadimawa da Ungwan Farinbatu.

Jiragen yakin NAF sun sake halaka yan bindiga masu yawa a Kaduna
Jiragen yakin NAF sun sake halaka yan bindiga masu yawa a Kaduna. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Damfarar N500,000: An yanke wa ma'aikacin gwamnatin Kano shekaru 5 a gidan ɗan kande

Saura sun hada da Sabuwa, Kutemeshi, Gajere, Sabon Kuyello, Dogon-Dawa, Ngade Allah, Kidandan da kuma wasu garuruwan da ke kananan hukumomin Birnin-Gwari da Giwa a jihar.

KU KARANTA: An rufe majalisar Ghana bayan mambobi da ma'aikata 168 sun harbu da korona

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da yan bindiga ke yawan kai hare hare a yankin Arewa.

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel