Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya dawo kan kafofin sada zumunta

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya dawo kan kafofin sada zumunta

- Bayan gargame asusun tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump, an sake bude masa

- Tsohon shugaban kasan ya dawo kan kafofin sada zumunta a matsayin tsohon shugaba

- Faceboo, Twitter, Instagram, Reddit, Snapchat da sauransu ne a baya suka gargame asusun

Donald Trump ya cire tsohuwar asusun Gab din sa saboda dawowar da ya yi ta kafofin sada zumunta sakamakon gogewar da manyan kamfanonin fasaha na Silicon Valley suka yi.

A sakonsa na farko zuwa shafin tun ranar 8 ga Janairu, Trump ya daura martanin lauyansa kan bukatun da ya bayar da shaida a sauraren tsige shi karo na biyu mako mai zuwa.

Trump ya koma ga sakin bayanan ne daga Ofishin tsohon shugaban kasar bayan da Facebook, Twitter, Instagram, Reddit, Snapchat, Twitch, Shopify, Stripe, da YouTube, da sauransu suka datse.

KU KARANTA: Kasuwancin kiwon shanu ya fi na kudin intanet, in ji Adamu Garba

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya dawo kan kafofin sada zumunta
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya dawo kan kafofin sada zumunta Hoto: The Verge
Asali: UGC

Duk da yake dawowarsa ga shafukan sada zumunta kawai ya sake rubuta wasikar lauyoyin nasa ne, kalmomin suna dauke da halayyar tsohon shugaban, kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito.

Lauyoyin David Schoen da Bruce Castor Jr sun rubuta cewa "Muna nan kan karbar sabuwar dangantakar ku ta jama'a."

“Wasikarku kawai ta tabbatar da abin da kowa ya sani ne: ba za ku iya tabbatar da zargin da kuke yi wa Shugaban Amurka na 45, wanda yanzu dan kasa ne mai zaman kansa.

"Amfani da Kundin Tsarin Mulkin mu wajen kawo karar da ake zargin tsige shi yana da matukar mahimmanci a yi kokarin yin wadannan wasannin.”

Lauyoyin Trump suna amsa jawabi ne daga dan majalisa Jamie Raskin cewa tsohon shugaban ya bayyana a gaba ko a lokacin shari’ar, kan batun yi masa tambayoyi, yana mai nuna shaidar tsoffin shugabanni Gerald Ford da Bill Clinton a lokacin da suke kan mulki.

KU KARANTA: Kano: Gwamna Ganduje ya gargadi malamai kan yin wa'azin batanci

A wani labarin, Donald Trump a ranarsa ta karshe a ofishin shugabancin Amurka ya yi wa sama da mutane 100 afuwa, ciki har da mawakn Amurka, Lil Wayne da Kodak Black.

Lil Wayne, wanda aka haifa Dwayne Michael Carter Jr, ya amsa laifinsa na mallakar haramtacciyar makami a jirgi mai zaman kansa yayin tafiya zuwa Miami a watan Disambar 2020, in ji rahoton Billboard.com.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel