Trump ya yi afuwa ga mawaki Wizzy a ranarsa ta karshe a ofis

Trump ya yi afuwa ga mawaki Wizzy a ranarsa ta karshe a ofis

- Shugaban kasar Amurka ya yi afuwa ga mutane sama da 100 ciki har da mawaki Lil Wayne

- Shugaban ya yi haka ne a ranarsa ta karshe na shugabancin kasar Amurka

- Mawaki Lil Wayne an kama shi da miyagun kwayoyi a cikin jirgi a hanyarsa ta Miami

Donald Trump a ranarsa ta karshe a ofishin shugabancin Amurka ya yi wa sama da mutane 100 afuwa, ciki har da mawakn Amurka, Lil Wayne da Kodak Black.

Lil Wayne, wanda aka haifa Dwayne Michael Carter Jr, ya amsa laifinsa na mallakar haramtacciyar makami a jirgi mai zaman kansa yayin tafiya zuwa Miami a watan Disambar 2020, in ji rahoton Billboard.com.

Carter mai laifi ne, wanda ya samo asali daga tuhumar bindiga a 2007, wanda ke nufin daurin shekaru 10 a kurkuku lokacin da za a yanke masa hukunci a Janairu 28, 2021.

KU KARANTA: Ba makarantu bane ke kara yaduwar cutar COVID-19 – UNICEF

Trump ya yafewa wani mawakin Amurka a ranarsa ta karshe a ofis
Trump ya yafewa wani mawakin Amurka a ranarsa ta karshe a ofis Hoto: Entertainment Weekly
Source: UGC

A ranar 23 ga Disamba, 2019, wani bayani da aka sakaya sunan mai shi ya jagoranci jami'an 'yan sanda na Miami da wakilan tarayya don bincika jirgin na Carter inda suka gano bindigar da aka loda.

An kuma gano hodar iblis, tabar wiwi, magunguna masu kashe zafin jiki da kuma maganin tari mai karfi, tare da kusan $26,000 a tsabar kudi. Ba a tuhumi Carter da duk wani laifin shan kwayoyi ba.

Hakanan, Kodak Black, wanda aka haifa Bill Kahan Kapri, yana gidan yarin tarayya bayan ya amsa laifin mallakar makamai bayan an tsare shi a kan iyakar Kanada da Amurka a watan Maris na 2020.

Trump ya kara yin afuwa ga tsohon manajan yakin neman zabensa Steve Bannon, tsohon Magajin Garin Detroit, Kwame Kilpatrick. Duk da haka, Wikileaks 'Julian Assange da Edward Snowden ba sa cikin jerin.

KU KARANTA: Dukkan kasashen Afrika na bukatar shugaba irin Buhari

A wani labarin, Jam’iyyar APC ta bukaci shugaban kasar Amurka Donald Trump da yayi koyi da takwaransa na Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), bayan faduwa zabe.

APC ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Sakataren ta Mai Kulawa da Kwamitin Shirye-shiryen Babban Taro, John Akpanudoedehe, mai taken, “Amincin shugaba yana da muhimmanci kamar cibiyoyi masu karfi’.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel