Kano: Gwamna Ganduje ya gargadi malamai kan yin wa'azin batanci
- Gwamnan jihar Kano ya gargadi malami da su daina yin wa'azin da zai ke tada hankali
- Gwamnan ya bayyana cewa addinin musulunci addini ne mai wanzar da zaman lafiya
- Ya kuma siffanta da'awar Annabi Muhammadu (S.A.W) da da'awar zaman lafiya da son juna
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya gargadi malaman addinin Islama da su daina yin kalamai masu tayar da hankali, wadanda za su iya keta zaman lafiya, yayin wa’azi, The Guardian ta ruwaito.
Ganduje ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a Kano lokacin da ya gana da Limamai na Masallacin Juma’at da sauran malaman addinin Musulunci a jihar.
Ya tunatar da malamai matsayinsu a cikin al'umma, yana mai cewa ya kamata su yi iya kokarinsu ko yaushe su zama abin koyi na fatar baki ko a aikace.
Ya kuma yi kira ga limamai su fito da hanyoyin da za su yada koyarwar addini na hakika.
KU KARANTA: 'Yan sandan Kaduna sun kame masu satar motoci, an kwato wasu motoci
"Annabi Muhammad ya yi wa'azin zaman lafiya, soyayya da hadin kai kuma a matsayinmu na mabiya addinin Musulunci na gaskiya, ya kamata mu yi koyi da irin wannan domin mu more rayuwa anan da kuma har abada," in ji shi.
Gwamnan ya bukaci ‘yan Najeriya su yi hakuri da juna, su zauna lafiya da juna, ba tare da la’akari da bambancin addini, al’adu da kabilanci ba.
Wata sanarwa da gwamnatin ta bayar ta umarci dukkan tashoshin watsa shirye-shirye da dandalin sada zumunta da su daina yada wa’azi, wa’azozi da duk wata tattaunawa ta addini da ka iya haifar da rashin zaman lafiya a jihar.
KU KARANTA: An kama wasu mutane huɗu da laifin noman tabar wiwi a jihar Ondo
Ta kuma umarci hukumomin tsaro da su tabbatar sun cika ka’ida tare da daukar kwararan matakai kan mutanen da suka yi kuskure ko kuma kungiyoyin da aka samu suna bijirewa umarnin.
A wani labarin, An ga jami'an tsaro masu yawa a kusa da gidan Sheikh Abdujabbar Nasiru Kabara a Gwale da ke karamar hukumar Gwale a cikin garin Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a safiyar yau Alhamis ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da dakatar da shahararren malamin addinin Islama din daga yin wa'azi a jihar saboda salon koyarwarsa da ake ganin yana da matukar tsanani.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng