Kasuwancin kiwon shanu ya fi na kudin intanet, in ji Adamu Garba

Kasuwancin kiwon shanu ya fi na kudin intanet, in ji Adamu Garba

- Wani tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya ya bayyana ra'ayinsa kan haramta kudin intanet a Najeriya

- Tsohon dan takarar ya ce kiwon shanu ya zarce sanya hannun jari a duk nau'ukan kudin intanet

- Ya kuma siffanta son banza da lalaci ke sanya matasa son zuba hannun jari a irin wannan kasuwanci

Tsohon dan takarar shugabancin Najeriya, Adamu Garba ya bayyana cewa saka hannun jari a kasuwancin kiwon shanu ya fi kowane nau'i na kasuwancin kudaden intanet da aka fi sani da cryptocurrency, PM News ta ruwaito.

Adamu ya fadi hakan ne yayin da yake maida martani ga umarnin da Babban Bankin Najeriya ya baiwa bankuna na rufe asusun mutane ko kuma wadanda suke da hannu a cikin hada-hadar kudi a cikin tsarin su.

Babban bankin a ranar Juma'a ya ba da wannan umarnin a cikin wata madauwari da aka fitar don ajiyar bankunan kudi (DMBs), cibiyoyin hada-hadar kudi na banki (NBFIs), da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi.

KU KARANTA: 'Yan sandan Kaduna sun kame masu satar motoci, an kwato wasu motoci

Kasuwancin kiwon shanu ya fi na kudin intanet, in ji Adamu Garba
Kasuwancin kiwon shanu ya fi na kudin intanet, in ji Adamu Garba Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

Yanayin da ya jawo cece-kuce a shafin twitter, mutane da dama sun bayyana ra'ayinsu dangane da wannan haramtawa da babban bankin Najeriya yayi.

A nasa bangaren, Adamu Garba ya bayyana cewa yafi kyau matasa su zuba hannun jari a fannin kiwon shanu fiye da zuba jari a irin wannan kasuwa na kudin gaibi.

Ya rubutu a shafin twitter dinsa cewa:

“Ingantaccen sa hannun jari! Waɗanda wataƙila zasu rasa kuɗaɗensu ta hanyar kasuwancin gajeriyar hanya da ake kira Crypto ya kamata su koyi saka hannun jari kan ainihin kadarori, kamar shanu, wanda ya ba da tabbacin samun riba mai tsoka kan saka hannun jari.
"Kasuwancin kiwon shanu ya fi riba fiye da duk abubuwan da ake haɗawa da cryptocurrencies.
Lol. "

KU KARANTA: Kano: Gwamna Ganduje ya gargadi malamai kan yin wa'azin batanci

A wani labarin, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya baiwa bankunan Najeriya umarnin rufe asusun 'yan kasuwa da kamfanoni masu amfani da kudin yanar gizo na cryptocurrency, matakin da bai yi wa dubban 'yan Najeriya dadi ba, BBC Hausa ta ruwaito.

Umarnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma'a ga bankunan hada-hadar kudi (DMB) da kamfanonin da ba na harkar kudi ba (NBFI) da kuma sauran ma'aikatun harkokin kudi a kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel