Ko shakka babu yan Najeriya za su sake zabar APC a 2023, in ji Hope Uzodinma

Ko shakka babu yan Najeriya za su sake zabar APC a 2023, in ji Hope Uzodinma

- Gwamna Hope Uzodinma ya nuna yakinin cewa APC za ta ci gaba da mulki a 2023

- Gwamnan na jihar Imo ya bayyana hakan yayinda jam’iyyar mai mulki ta kaddamar da shirin yiwa mambobinta rijista

- Gwamna Uzodinma ya kuma bayyana cewa APC ba za ta yi sanyi ba idan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar mulki

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya kaddamar da cewar yan Najeriya za su sake zabar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a zaben 2023.

Uzodinma ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da Channels Television a ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Shahararren malamin Musulunci Sheikh Gumi ya yi babban hasashe kan fashi a arewa

Ko shakka babu yan Najeriya za su sake zabar APC a 2023, in ji Hope Uzodinma
Ko shakka babu yan Najeriya za su sake zabar APC a 2023, in ji Hope Uzodinma Hoto: @GovtOfImoState
Asali: Facebook

Furucinsa:

“Duba ga ayyuka da nasarorin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, babu tantama cewa yan Najeriya za su sake zabar APC.”

Wasu yan Najeriya a shafin Twitter na ta martani a kan furucin gwamnan na jihar Imo.

KU KARANTA KUMA: Jami’ar Al-Qalam da wasu jami’o’i masu zaman kansu guda 98 a Nigeria

Ogar Owogaga ya rubuta:

“A mafarkinka! Ci gaba da mafarki!”

Yahaya Wada ya rubuta:

“APC bata da kishiya a 2023. Gwamna Uzodinma ya yi gaskiya.”

Godstime Eribo ya rubuta:

“Idan baki ne wannan, na ce ba zai kama mu ba, kuma hakan ba zai kasance ba.”

A wani labarin kuma, Bashir Bolarinwa, shugaban riko na jam’iyyar APC a Kwara ya bada labarin yadda aka auka masu da hari a wajen zaman jam’iyya da aka kira a Ilorin.

Bashir Bolarinwa ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan an kira su zuwa wajen rajistar da kwamitin Sanata John Danboyi ya ke yi a dakin taro na Banquet Hall.

A cewar Bolarinwa, har zuwa karfe 1:30 na rana, ba a bude wurin da aka ce za ayi taro da karfe 12:00 ba. Wannan ya sa a aikawa Sanata Danboyi sako ta wayar salula.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng