Hawaye sun kwaranya yayinda tsohon dan majalisa Maikano Rabiu ya rasu

Hawaye sun kwaranya yayinda tsohon dan majalisa Maikano Rabiu ya rasu

- Allah ya yi wa Alhaji Abdullahi Maikano Rabiu rasuwa

- Tsohon dan majalisar ya rasu a ranar Alhamis yana da shekaru 72 a jihar Kano

- Rabiu, wanda za a binne daidai da koyarwar addinin Islama, ya rasu ya bar yan uwa, yara da mata

Mutanen karamar hukumar Dawakin Tofa da ke jihar Kano sun shiga halin juyayi sakamakon mutuwar tsohon dan majalisa, Dr Abdullahi Maikano Rabiu.

A cewar jaridar The Punch, tsohon dan majalisan wakilan ya rasu sakamakon cutar COVID-19 a ranar Alhamis, 4 ga watan Fabrairu.

Rabiu ya rasu a cibiyar killace masu cutar da ke Kwanar Dawakin Tofa, a Kano, inda yan uwansa suka tabbatar da mutuwarsa ga manema labarai a ranar Alhamis.

Hawaye sun kwaranya yayinda tsohon dan majalisa Maikano Rabiu ya rasu
Hawaye sun kwaranya yayinda tsohon dan majalisa Maikano Rabiu ya rasu Hoto: Maikano Rabiu Foundation
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: Ko shakka babu yan Najeriya za su sake zabar APC a 2023, in ji Hope Uzodinma

“Tare da nauyin zuciya da tawakkali ga Allah madaukakin sarki muna bakin cikin sanar da mutuwar shugaba kuma ma’assashin wannan gidauniya. Muna addu’a kan Allah ya yafe masa zububansa da kuma bashi babban wuri a Al-jannah madaukakiya. Allah ya sa ka huta Dallatu.”

Rabiu wanda ya kasance tsohon mai ba tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau shawara kan harkokin tattalin arziki ya riki mukaman siyasa da dama a rayuwarsa.

Ya mutu yana da shekaru 72 a duniya kuma za a binne shi daidai da koyarwar addinin Musulunci a garinsa na Dawakin Tofa.

Tsohon dan majalisar ya mutu ya bar matar aure daya, yara da yan uwa.

KU KARANTA KUMA: Shahararren malamin Musulunci Sheikh Gumi ya yi babban hasashe kan fashi a arewa

A wani labarin kuma, mun ji cewa Alhaji Isa Ibrahim, kawun ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Nigeria, Sheikh Dr. Isa Ali Pantami ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne a ranar Laraba 3 ga watan Fabrairun shekarar 2021 a garin Gombe bayan gajeruwar rashin lafiya kamar yadda ministan ya sanar a shafinsa na Twitter.

Ya yi addua'ar Allah ya jikansa da rahama ya gafarta masa kurakurensa da ma sauran iyaye da yan uwa da suka rasu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel