Boko Haram sun kashe 'yan sanda 2, sun sace 2 yayin da sabbin hafsoshin tsaro ke Borno

Boko Haram sun kashe 'yan sanda 2, sun sace 2 yayin da sabbin hafsoshin tsaro ke Borno

- Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari Chabal da wasu anguwannin Magumeri dake jihar Borno

- Al'amarin ya faru ne a ranar Lahadi wanda yayi sanadiyyar mutuwar 'yan sanda biyu tare da sace biyu

- Sun kuma banka wa motocin sintiri biyu wuta da kuma wani a kan hanyar Maiduguri-Chabal -Magumeri

Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun afka Chabal da wasu anguwanni dake karkashin karamar hukumar Magumeri a ranar Lahadi da rana sannan sun kashe wasu 'yan sanda guda biyu kafin su yi garkuwa da wasu biyu.

Kamar yadda wasu suka sanar da Vanguard, 'yan ta'addan sun kwace wasu motocin sintiri guda biyu sannan suka banka wa daya wuta a hanyar Maiduguri-Chabal-Magumeri titi mai tsawon 35km arewa da babban birnin jihar.

Al'amarin ya faru ne bayan sababbin hafsoshin sojin Najeriya da sun kai ziyara Maiduguri, inda suka kai wa gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ziyara da Shehun Borno, Abubakar Garbai Elkanemi don neman hadin kansu wurin kawo karshen rikici a jihar.

Sai ga 'yan ta'adda sun kai farmaki jihar a yau Lahadi.

KU KARANTA: Gwamnan APC ya amince da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, rai da rai ga masu fyade

Boko Haram sun kashe 'yan sanda 2, sun sace 2 yayin da sabbin hafsoshin tsaro ke Borno
Boko Haram sun kashe 'yan sanda 2, sun sace 2 yayin da sabbin hafsoshin tsaro ke Borno. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram sun kai hari Dikwa, sun ce sabbin hafsin soji basu isa su hana su komai ba

A wani labari na daban, wasu matasa sun kai wa kwamishinan ayyukan jihar Ondo, Saka Ogunleye, farmaki yayin da rikicin cikin jam'iyyar APC yake kara ruruwa a tsakanin 'yan jam'iyyar.

Ana zargin karamin ministan Niger Delta, Chief Tayo Alasoadura da tura matasan don su kai wa kwamishinan farmaki.

Dama rikici ya balle tsakanin kwamishinan da karamin ministan, wanda ake zargin haka ne makasudin da ya sanya ministan sanya matasan kai wa kwamishinan farmaki a garin Iju ana tsaka da taron rijista da tabbatar da 'yan jam'iyyar APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel