Bata-gari sun kai wa kwamishina hari, sun hargitsa wurin rijistar jam'iyyar APC

Bata-gari sun kai wa kwamishina hari, sun hargitsa wurin rijistar jam'iyyar APC

- Wasu 'yan daban matasa sun kai wa kwamishinan ayyuka na jihar Ondo, Saka Ogunleye, farmaki

- Ana zargin karamin ministan Niger Delta, Chief Tayo Alasoadura ne ya sanya matasan su kai masa farmakin saboda sun samu sabani

- Ana tsaka da taron tattaunawa akan cigaban jam'iyyar kwatsam sai ga matasan da miyagun makamai inda suka yi kaca-kaca da wurin

Wasu matasa sun kai wa kwamishinan ayyukan jihar Ondo, Saka Ogunleye, farmaki yayin da rikicin cikin jam'iyyar APC yake kara ruruwa a tsakanin 'yan jam'iyyar.

Ana zargin karamin ministan Niger Delta, Chief Tayo Alasoadura da tura matasan don su kai wa kwamishinan farmaki.

Dama rikici ya balle tsakanin kwamishinan da karamin ministan, wanda ake zargin haka ne makasudin da ya sanya ministan sanya matasan kai wa kwamishinan farmaki a garin Iju ana tsaka da taron rijista da tabbatar da 'yan jam'iyyar APC.

KU KARANTA: Kotun Amurka za ta kwace dukiyar tsohuwar budurwar Dangote, ta saka mata sharadi

Bata-gari sun kai wa kwamishina hari, sun hargitsa wurin rijistar jam'iyyar APC
Bata-gari sun kai wa kwamishina hari, sun hargitsa wurin rijistar jam'iyyar APC. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Taron da shugaban jam'iyyar na Akure ta arewa, Joshua Eleti, ya shirya don tattaunawa akan yadda za a fara rijistar a ranar 2 ga watan Fabrairu, kwatsam sai ga matasan da miyagun makamai.

Take anan suka kai wa masu ruwa da tsakin jam'iyyar farmaki, yayin da wasu suka tsere cikin tsananin tsoro, Vanguard ta wallafa.

Kamar yadda rahotonni suka gabata, matasan sun kai wa kwamishinan farmaki. Sannan sai da suka ji wa sauran wadanda suka raka kwamishinan munanan raunuka.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Ka bai wa sabbin hafsoshin tsaro wa'adin kawo canji, Ndume

A wani labari na daban, 'yan majalisa bakwai na jihar Ogun da suka hada da shugaban marasa rinjaye, Ganiyu Oyedeji ne suka bar jam'iyyar APM zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Kakakin majalisar jihar, Olakunle Oluomo, ya bayyana haka a wasu wasiku mabanbanta da ya karanta yayin zaman majalisar a ranar Alhamis a Abeukuta, babban birnin jihar, Punch ta wallafa.

Wadanda suka sauya shekar baya da Oyedeji: Musefiu Lamidi (Ado Odo Ota 11), Yusuf Amosun (Ewekoro), Sikiratu Ajibola (Ipokia), Bolanle Ajayi (Yewa South), Adeniran Ademola (Sagamu 11) da Modupe Mujota-Onikepo (Abeokuta North).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel