Boko Haram sun kai hari Dikwa, sun ce sabbin hafsin soji basu isa su hana su komai ba

Boko Haram sun kai hari Dikwa, sun ce sabbin hafsin soji basu isa su hana su komai ba

- Mayakan ta'addancin Boko Haram sun kai gagarumin hari garin Dikwa da ke Borno

- Wannan harin yana zuwa ne kasa da sa'o'i 24 bayan mika ragamar mulkin ga sabon hafsin soji Attahiru

- Mazauna garin Dikwa sun dinga tserewa zuwa dajikan da ke da kusanci da su domin tseratar da rayukansu

Kasa da sa'o'i 24 bayan fara aikin sabon shugaban hafsin sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, mayakan ta'addanci na Boko Haram sun kai hari garin Dikwa da ke karamar hukumar Dikwa ta jihar Borno.

Bayan maye gurbin shugabannin tsaro na kasar nan a ranar Talata, shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya yi bidiyo cike da takama inda yace sabbin hafsoshin tsaron ba za su iya yin komai a kansu ba.

An gano cewa mayakan ta'addancin masu tarin yawa sun tsinkayi garin Dikwa a motocin yaki inda suka yi musayar wuta da dakarun soji yayin da mazauna garin suka dinga tserewa daji.

KU KARANTA: Magidanci ya gurfana a gaban kotu bayan yayi garkuwa da 'ya'yansa 2

Boko Haram sun kai hari Dikwa, sun ce sabbin hafsin soji basu isa su hana su komai ba
Boko Haram sun kai hari Dikwa, sun ce sabbin hafsin soji basu isa su hana su komai ba. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: Facebook

Mazauna yankin da suka tsere zuwa daji sun sanar da Vanguard cewa mayakan ta'addancin sun kai gagarumin hari Dikwa kuma harbe-harbe ne yasa suka tsere.

Dikwa tana da nisan kilomita 60 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Yana da kusanci da karamar hukumar Mafa, asalin garin Gwamna Babagana Zulum.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya mika bukatar tabbatar da sabbin hafsoshin tsaro ga majalisa

A wani labari na daban, dakarun sojin saman Najeriya a ranar Alhamis sun kashe 'yan bindiga masu yawa a samamen da suka kai ta jiragen yaki a kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun.

Kwamishinan tsaro na cikin gida, Samuel Aruwan, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis, Premium Times ta wallafa.

Ya ce yankunan da aka yi wannan aikin sun hada da babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari, Buruku, Ungwar Yako, Udawa, Polewire, Crossing Point, Gagafada, Kugu, Kamfani Doka, Gwaska, Goron Dutse da yankunan masu kusanci da nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: