Dakarun rundunar sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram, sun kashe mutum 5

Dakarun rundunar sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram, sun kashe mutum 5

- Rundunar sojin Najeriya ta Operation Tura Takaibango ta kashe yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno

- Sojojin sun kuma yi nasarar lalata mabuya da kayayyakin yan ta'addan a farmakin da suka kai masu

- Hedkwatar rundunar tsaro ta kasa ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter

Hedlkwatar tsaro ta ce dakarun Operation Tura Takaibango sun halaka yan Boko Haram biyar a kokarinsu na ketare garuruwan Abbagajiri da Dusula da ke karamar hukumar Damboa na jihar Borno.

Birgediya Janar, Benard Onyeuko, mukaddashin darakta na ayyukan tsaro, a wani jawabi a ranar Juma’a, ya ce dakarun sun yi gagarumin nasara a kan yan ta’adda a arewa maso gabas.

Onyeuko ya ce dakarun tawaga ta musamman na 402 a ranar Laraba, sun gano tare da kewaye wasu yan bindiga a Abbagajiri sannan suka bude masu wuta.

Dakarun rundunar sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram, sun kashe mutum 5
Dakarun rundunar sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram, sun kashe mutum 5 Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

A cewarsa, a karshen arangaman, an kashe yan ta’addan Boko Haram biyar yayinda wasun su suka tsere da raunukan harbi.

Ya bayyana cewa dakarun sun kuma kwato wani bindigar Pulenyot Kalashnikova Tankovyy (PKT), bindigogin AK-47 uku, wasu mujallar bindigogin AK-47.

KU KARANTA KUMA: Da’awar zaman lafiya: Malaman Kirista na arewa sun jinjinawa Sheikh Gumi

Onyeuko ya kara da cewa an kuma kama tare da lalata wasu kayan hada bama-bamai da sauransu.

Ya ce sabon farmakin da dakarun ke kaiwa sauran yan Boko Haram na nuna kawo karshen duk wasu yan ta’adda a arewa maso gabas.

A cewarsa, dakarun Operation Tura Takaibango sun cancanci jinjina kan jajircewa da kokarinsu na kakkabe sauran yan ta’addan daga mabuyarsu.

“An kuma karfafa masu gwiwar cewa kada su yi kasa a gwiwa illa kara bunkasa nasarar da suka samu.

“Don haka ana ba dukkanin mutanen arewa maso gabas tabbacin sabonta kokarin rundunar sojin Najeriya don rugurguza sauran yan Boko Haram daga mabuyarsu a yankin nan,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Kyaftin din Super Eagles Musa ya nuna motocin alfarma da ke garejinsa na N200m yayin da ya nufi masallaci

A wani labarin, dakarun sojojin Najeriya bakwai ne 'yan bindiga suka kashe yayin wani arangama da suka yi a hanyar Mararaba-Udege a karamar hukumar Nasarawa ta Jihar Nasarawa kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sojojin da ke 177 Guard Battalion na barikin Shitu Alao da ke Keffi a Jihar Nasarawa sun rasu ne sakamakon harin kwantar bauna da 'yan bindigan suka yi musu.

A cewar majiya kwakwara wanda bai so a ambaci sunansa saboda dalilan tsaro, sojojin da suka mutu suna cikin tawagar sojoji 13 ne da Kyaftin Felix Kura ya yi wa jagora zuwa dajin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel