Kyaftin din Super Eagles Musa ya nuna motocin alfarma da ke garejinsa na N200m yayin da ya nufi masallaci

Kyaftin din Super Eagles Musa ya nuna motocin alfarma da ke garejinsa na N200m yayin da ya nufi masallaci

- Ahmed Musa ya nufi masallaci kamar yadda ya bayyana a wani hoto da ke nuna tsadaddun motocinsa a baya

- An tattaro cewa kyaftin din na Super Eagles na da motoci da ya kai akalla naira miliyan 200 a garejinsa

- A sabon wallafarsa, matashin mai shekaru 28 ya yi addu’o’i domin karfafa wa masoyansa gwiwa

A matsayinsa na jajirtaccen Musulmi, an gano kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa a cikin wani hoto ya nufi masallaci don yin sallah, inda kasan hoton ya hasko garejinsa.

An tattaro cewa Musa, wanda ya bar kungiyar kwallon kafa na Al Nassr na kasar Saudiyya a shekarar bara, yana da akalla motocin da ya kai naira miliya 200 a garejinsa.

A wallafar da yayi a ranar Juma’a, 22 ga watan Janairu, Musa ya bar zantuka na addu’o’i ga mabiyansa inda yayi addu’an cewa Allah zai bude masu kofofin samu.

Kyaftin din Super Eagles Musa ya nuna motocin alfarma da ke garejinsa na N200m yayin da ya nufi masallaci
Kyaftin din Super Eagles Musa ya nuna motocin alfarma da ke garejinsa na N200m yayin da ya nufi masallaci Hoto: Laurence Griffiths
Asali: Getty Images

KU KARANTA KUMA: FG ta bayar da sabon bayani kan shirin bayar da tallafin kudi ga matasa (kalli lambobin wayar kowani yanki)

Ya rubuta:

"Allah Madaukakin Sarki kar ya taba bari zuciyarku ta rikice da jarabawar rayuwa.

"Allah ya ci gaba da bude mana kofofin Rahamarsa, ya saukaka hanyoyinmu, ya karbi ibadunmu, ya albarkaci karshenmu, ya sanyaya kaburburanmu, ka gafarta mana zunubanmu da na iyayenmu kuma daga karshe ka maida Jannatul Firdaus gidanmu na karshe Ameen. Jummat Mubarak. "

KU KARANTA KUMA: COVID-9: Kada ka yi wasa da rayukan mutanenka, Kungiyar NGF ta gargadi wani babban gwamnan Nigeria

Tsohon dan wasan gaba na Leicester City mai shekaru 28 da haihuwa ya kasance mai matukar birgewa da ayyukansa na jin kai a fadin kasar.

Bayan kammala wajen wasanni biyu masu kayatarwa a Kano da Kaduna, dan wasan ya bayyana shirinsa na gina ingantaccen makaranta a Jos.

A wani labarin, an nuna gidan da sabuwar mataimakiyar kasar Amurka, Kamala Harris za ta zaune tare da iyalanta na tsawon shekaru hudu a wa'addin mulkinta.

Harris a ranar Laraba 20 ga watan Janairun 2021 ta kafa tarihi ta zama mace na farko kuma bakar fata da ta zama mataimakiyar shugaban kasar Amurka.

Harris, mai shekaru 56 za ta tare a gidan da ke Naval Observatory a arewa maso yamman Washington DC a gidan da magabatanta suka zauna shekaru da dama da suka shude.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng