Da’awar zaman lafiya: Malaman Kirista na arewa sun jinjinawa Sheikh Gumi

Da’awar zaman lafiya: Malaman Kirista na arewa sun jinjinawa Sheikh Gumi

- Malaman addinin Kirista a arewacin kasar sun jinjinawa Sheikh Ahmad Gumi kan da'awar zaman lafiya da yake yawon yi a dazukan Kaduna

- Gumi dai na bi mazaunin yan ta'adda yana wayar masu da kai a kan bukatar rungumar zaman lafiya a kokarinsa na kawo karshe kashe-kashe da fashi a Kudancin Kaduna

- Fasto Yohanna Baru ya ce yunkurin Gumi na yin da'awar zai taimaka sosai wajen daidaita matsalar tsaro a kasar

Kungiyar malaman Kirista na arewa sun yaba da kokarin da Sheikh Ahmad Gumi ke yi wajen samo mafita mai dorewa kan rashin tsaro a jihar Kaduna, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, Sabon Tasha, Kaduna, Fasto Yohanna Baru ya ce yunkurin Gumi na shiga dazukan Kudancin Kaduna don zantawa da makiyaya kan muhimmancin zaman lafiya da hadin kan kasar ya cancanci jinjina.

KU KARANTA KUMA: Kyaftin din Super Eagles Musa ya nuna motocin alfarma da ke garejinsa na N200m yayin da ya nufi masallaci

Da’awar zaman lafiya: Malaman Kirista na arewa sun jinjinawa Sheikh Gumi
Da’awar zaman lafiya: Malaman Kirista na arewa sun jinjinawa Sheikh Gumi Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

A cewarsa:

“Allah ne kadai zai saka ma malamin Musuluncin a kan sadaukar da lokacinsa da yayi wajen ziyartan Fulani a jeji, sannan ya ja hankalinsu kan bukatar su karbi addinin Islama da ilimin zamani tare da kiwon dabbobi.

“Shi na daban ne kuma ya banbanta a tsakanin dukkan malamai da tsarinsa na kawo karshen kashe-kashe, fashin shanu, garkuwa da mutane, fashi da makami da sauransu.

"Don haka ya zama dole mun jinjina masa kan daukar wannan babban mataki da yayi wajen sasanci da ilimantar da matasan Fulani kan hatsarin da ke cikin ta’ammali da kwayoyi da aikata ta’addanci.”

KU KARANTA KUMA: COVID-9: Kada ka yi wasa da rayukan mutanenka, Kungiyar NGF ta gargadi wani babban gwamnan Nigeria

Buru ya kara da cewa: “ba za a taba dauke kai ga muhimmancin zaman lafiya ba, saboda haka akwai bukatar su rungumi zaman lafiya, hadin kai da sasanci tare da gwamnati don magance masu matsalolinsu a kokarin kawo ci gaba a kasar.”

Ya kuma yi kira ga malaman Musulunci da su yi koyi da kokarin Gumi sannan su samu lokaci don ziyartan Fulanin da ke zama a jeji don ilimantar da su da wayar masu da kai kan zaman lafiya.

Ya kuma yi kira ga kungiyar Jama’atu Nasril Islam da majalisar limamai da malamai a kasar da su hada hannu da Sheikh Gumi wajen tallata zaman lafiya ya mutanen da ke zama a jeji.

Hakazalika, Wani malamin Kirista, Reverend Paul Elisha Ham, ya roki masu hannu da shuni, shugabannin tsaro, kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wa malamin Musuluncin wajen yada da’awar zaman lafiya a fadin jihohin arewa 19 da ke kasar.

Ya kuma bukaci gwamnatin jihar Kaduna da ta tallafa wa malamin da isasshen tsaro a duk lokacin da zai je jeji don yin da’awah.

A wani labarin, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya tuhumci wasu sarakunan gargajiya a jihar da yiwa gwamnatinsa zagon kasa wajen kokarin kawo karshen matsalar tsaron jihar.

Gwamnan, a wata ganawa da yayi da shugabannin hukumomin tsaro a jihar ranar Alhamis, ya ce sarakunan gargajiya ba sa taka nasu rawan wajen yaki da yan bindiga.

Ya ce hakan ya sa matsalar tsaro ta kara tsanani a jihar kwanakin nan, Premium Times ta ruwaito.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel