Sojojin Nigeria 7 sun gamu da ajalinsu a hannun 'yan bindiga a dajin Nasarawa

Sojojin Nigeria 7 sun gamu da ajalinsu a hannun 'yan bindiga a dajin Nasarawa

- Sojojin Najeriya bakwai sun riga mu gidan gaskiya sakamakon arangama da 'yan bindiga a Nasarawa

- Rahotanni sun ce an tura sojojin dajin ne domin ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su ashe tarko 'yan bindiga suka shirya musu

- Kakakin rundunar sojojin Najeriya, Brigediya Janar, Sagir Musa, ya ce ba shi da masaniya a kan afkuwar lamarin

Dakarun sojojin Najeriya bakwai ne 'yan bindiga suka kashe yayin wani arangama da suka yi a hanyar Mararaba-Udege a karamar hukumar Nasarawa ta Jihar Nasarawa kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sojojin da ke 177 Guard Battalion na barikin Shitu Alao da ke Keffi a Jihar Nasarawa sun rasu ne sakamakon harin kwantar bauna da 'yan bindigan suka yi musu.

Sojojin Nigeria 7 sun gamu da ajalinsu a hannun 'yan bindiga a dajin Nasarawa
Sojojin Nigeria 7 sun gamu da ajalinsu a hannun 'yan bindiga a dajin Nasarawa. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sunyi alkawarin ajiye makamai bayan Gumi ya bi su garuruwansu ya musu wa'azi

A cewar majiya kwakwara wanda bai so a ambaci sunansa saboda dalilan tsaro, sojojin da suka mutu suna cikin tawagar sojoji 13 ne da Kyaftin Felix Kura ya yi wa jagora zuwa dajin.

Majiyar ya ce an tura sojojin dajin ne domin ceto wasu mazauna jihar da 'yan bindigan suka sace kuma suka shiga da su cikin daji.

Daga cikin sojojin 14, Premium Times ta ruwaito cewa bakwai cikinsu har da Mista Kura; Yakubu Bati, mai mukamin saja; Kefas Iliya, lance corporal, da wasu hudu da ba a tabbatar da sunansu ba a lokacin hada wannan rahoton duk sun mutu.

"Suna shiga dajin nan take suka gano cewa gadar-zare aka shirya musu sannan suka lura an fi su yawa, an ce Mista Kura ya fada wa abokan aikinsa har da mai tsaronsa su fice daga dajin," a cewar majiyar.

KU KARANTA: Gwamnatin Jihar Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki

Majiyar Legit.ng ta ce ta gano an sanar da iyalan sojojin da suka rasu an kuma tura sako hedkwatar sojoji na kasa.

Amma mai magana da yawun rundunar sojoji, Sagir Musa, mai mukamin brigediya janar, ya ce bai da masaniya kan afkuwar lamarin.

"Bani da masaniya. Ban san wani abu mai kamar haka ya faru ba," Mista Musa ya shaidawa wakilin Premium Times a wayar tarho a ranar Alhamis.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164