Wanda na fara sace wa shine tsohon saurayi na da ya ƙi aure na, in ji mai garkuwa, Maryam
- Wata mai garkuwa da mutane Maryam, ƴar shekara 23 ta ce tsohon saurayin ta da ya guje ta ta fara sacewa
- Ta bayyana yadda kawunta ya jefa ta a harkar garkuwa da mutane bayan saurayin yaki auren ta bayan tayi kokarin shawo kansa
- Daga cikin kudin fansar da aka bata tayi amfani da shi wajan kama hayar gidan zama a Kano
Rundunar yan sandan Jihar Kano a ranar Laraba ta cafke wasu masu garkuwa da mutane su hudu cikin su har da mace ƴar shekara 23, Maryam Mohammed, Daily Trust ta ruwaito.
Ta shaida cewa aikin ta na farko a matsayin mai garkuwa da mutane ya fara ta kan tsohon saurayin ta wanda yaki auren ta bayan shafe shekaru suna soyayya.
DUBA WANNAN: Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa
Maryam Mohammed, wanda aka fi sani da Hajiya, an kama ta a ranar Talatar da ta gabata tare da wasu mutane uku yan tawagar ta a unguwar Jaba, karamar hukumar Ungogo da ke Jihar Kano, lokacin da suke tattaunawa da iyalan daya daga cikin wanda suka sace akan kudin fansa.
Ta ce kawun ta ne ya fara jefa ta a harkar, wani Hamza Dogo na kauyen Butsa, karamar hukumar Gusau a Jihar Zamfara, bayan sun rabu da tsohon saurayin ta.
"Kawu na, da ake kira Hamza, dan garin Butsa, karamar hukumar Gusau a Jihar Zamfara kuma wanda muka fara garkuwa da shi tsohon saurayi na ne wanda ya ƙi aure na duk da ƙoƙarin da na yi na shawo kansa yayin soyayyar mu.
KU KARANTA: 'Yar shugaban Amurka Trump za ta auri saurayinta da ya girma a Nigeria
"Bayan ya guje ni, kawu na ya sa na kawo shi ta yadda zamu rike shi har sai ya biya mu wasu kudade kafin mu sake shi.
"Da muka yi garkuwa da shi, iyalan sa sun biya miliyan 5 don kwato shi, kuma an bani 800,000 daga ciki wanda nayi amfani da su wajen hayar gida a unguwar Jaba" in ji Hajiya.
An ruwaito tawagar a matsayin daya daga cikin masu sace sacen mutane a Kano da Zamfara.
Kakakin rundunar yan sandan Jihar Kano ya ce bayan sun yi bincike sun gano mijin ta wani barawon shanu ne, Sani Ismail, dan asalin Bida wanda aka kashe a ƙauyen Butsa bayan ya sato wani garken shanu.
Ta zauna a unguwaninnin Panshekara, Medile da Unguwa Uku kafin ta koma Jaba.
A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng