Karyata COVID-19: Gwamnan Kogi na bukatar ayi masa karatun ta natsu, Farfesa

Karyata COVID-19: Gwamnan Kogi na bukatar ayi masa karatun ta natsu, Farfesa

- Gwamnan jihar Kogi ya bukaci jama'ar Nigeria su bude idonsu da kyau kafin karbar allurar rigakafin kwayar cutar korona

- A cewar Bello, an kirkiri rigakafin korona cikin kankanin lokaci amma har yanzu ba'a kirkiro rigakafin wasu manyan cututtuka irinsu kanjamau da zazzabin cizon sauro ba

- Sai dai, wata farfesa mai ta caccakesa inda tace yana bukatar a karantar da shi

Wata Farfesar ilmin hada magunguna, Chinedum Babalola, ta caccaki gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, inda ta ce shi kanshi gwamnan na bukatar ya natsu a karantar da shi kan cutar COVID-19.

Farfesa Babalola, wacce ita ce shugabar jami'ar Chrisland Abeokuta, ya ce maganan Yahaya Bello ya nuna cewa ya jahilci lamarin cutar, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarta, ana bukatar ilmantar da jama'a sosai kan rigakafin cutar Korona.

"Wannan wayar da kan daga sama ya kamaya a fara. Idan gwamna zai iya magana haka, ya zama wajibi a ilmantar da shi yadda ya kamata. COVID-19 na kashe mutane, na rasa abokan aiki. Na rasa abokai sakamakon COVID-19," Farfesar ta bayyana.

KU KARANTA: Jami'an Sojojin Najeriya dake faggen fama 127 sun ajiye aiki

Karyata COVID-19: Gwamnan Kogi na bukatar ayi masa karatun ta natsu
Karyata COVID-19: Gwamnan Kogi na bukatar ayi masa karatun ta natsu
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan damfara da sunan COVID-19 sun bayyana a birnin Abuja, FCTA

Hakazalika wata kungiya mai rajin kare martabar jam'iyyar APC ta soki gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, akan kalamansa da ke sukar rigakafin allurar kwayar cutar korona.

A cewar kungiyar (APC Mandate Defenders) Kalaman gwamna Yahaya Bello daidai suke da tunzura jama'a domin tozarta shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kamar yadda TheNews ta wallafa.

Kungiyar ta bayyana cewa hankalinta ya kai kan wani faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo inda aka ji Gwamnan na fadawa magoya bayansa kar su yarda da rigakafin saboda tana kisa.

A wani jawabi da sakataren yada labarai, Ifeanyi Emeka, ya fitar, kungiyar ta bayyana cewa; "mun yarda cewa gwamna Bello yana da 'yancin bayyana wautarsa amma ya sani cewa ba za'a zuba masa ido ya tsallake makadi da rawa ba, wautarsa ta tsaya iya kansa.

A wani labarin kuwa, Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya saki matarsa ta uku mai suna Hafiza a cewar wasu rahototanni.

Vanguard ta ruwaito cewa an tabbatar da hakan kwanaki kadan da suka wuce a jawabin da ya yi yayin da ya ke karbar lambar yabo daga Cibiyar Kungiyoyin Mata na Kasa (NCWS).

Asali: Legit.ng

Online view pixel