Jami'an Sojojin Najeriya dake faggen fama 127 sun ajiye aiki

Jami'an Sojojin Najeriya dake faggen fama 127 sun ajiye aiki

- Wasu jami'an Sojojin Najeriya sun nemi fita daga gidan soja

- Hukumar bata bayyana dalilin da ya sa jami'an Sojojin suka bukaci ajiye aikin ba

- Najeriya na fama da matsalar rashin tsaro a daukacin Arewacin Najeriya

Jami'an Sojojin Najeriya 127 na hanyarsu ta fita daga hukumar duk da tsanantan lamarin tsaro a Najeriya da kuma kalubalen da ake fuskanta wajen yaki da yan bindiga a fadin tarayya.

Sojojin, dukkansu masu kananan mukamai ne daga sassan hukumar daban-daban kuma masu yaki a faggen fama.

Sojojin sun hada da Master Warrant Officer 1, Warrant Officer 3, 22 Staff Sajen 22, Sajen 29, Kofur 64, Lance Kofur 7 da Private 1, Premium Times ta ruwaito.

Wadanda sojoji zasu ajiye aiki ne a watan Mayun shekarar nan.

Babban hafsan sojin kasa, Laftanan Janar Tukur Buratai, ya amince da ajiye aikinsu.

Jerin Sojojin bai bayyana dalilin da yasa suka yanke shawaran fita daga gidan soja ba.

A cewar takardar da Birgediya Janar T.A Gagariga ya rattafa hannu, an bukaci dukkan Sojojin 127 su ajiye dukkan dukiyoyin hukumar dake hannunsu.

"Bisa sashe na A, babban hafsan Sojin kasa ya amince da fitar wadannan Sojojin da aka ambata sama NWO da wasu 126. Sojojin zasu tafi hutu a ranar 26 ga Afrilu, 2021, yayinda zasu ajiye aikin ranar 26 ga Mayu 21 bisa dokokin gidan Soja na 27, sakin layi na 3 da 4," takardar ya laburta.

DUBA NAN: Uwargidar Zakzaky, Hajiya Zeenatu, ta kamu da Coronavirus

Jami'an Sojojin Najeriya dake faggen fama 127 sun ajiye aiki
Jami'an Sojojin Najeriya dake faggen fama 127 sun ajiye aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da aka yiwa masu batanci ga Annabi 2 a Kano

A wani labarin kuwa, hedikwatar rundunar tsaro ta kasa (DHQ) ta musanta rahotannin kafafen yada labaran da suka bayyana cewa an samu galaba akan rundunar sojin Najeriya yayi harin garin Marte.

A ranar 15 da 16 ga watan Janairu ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari sansanin sojoji da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno.

Janar John Enenche, shugaban sashen yada labari na rundunar tsaro ta kasa, ya ce mayakan kungiyar Boko Haram/ISWAP sun kai farmaki sansanin soji da ke wajen garin Marte, amma an dakile harin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel