An gargadi gwamna Yahaya Bello akan sukar allurar rigakafin cutar korona

An gargadi gwamna Yahaya Bello akan sukar allurar rigakafin cutar korona

- Gwamnan jihar Kogi ya bukaci jama'ar Nigeria su bude idonsu da kyau kafin karbar allurar rigakafin kwayar cutar korona

- A cewar Bello, an kirkiri rigakafin korona cikin kankanin lokaci amma har yanzu ba'a kirkiro rigakafin wasu manyan cututtuka irinsu kanjamau da zazzabin cizon sauro ba

- Sai dai, wata kungiya mai rajin kare martabar APC ta ce ba zata bari wautar Gwamnan ta wuce iya kansa shi kadai ba

Wata kungiya mai rajin kare martabar jam'iyyar APC ta soki gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, akan kalamansa da ke sukar rigakafin allurar kwayar cutar korona.

A cewar kungiyar (APC Mandate Defenders) Kalaman gwamna Yahaya Bello daidai suke da tunzura jama'a domin tozarta shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kamar yadda TheNews ta wallafa.

Kungiyar ta bayyana cewa hankalinta ya kai kan wani faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo inda aka ji Gwamnan na fadawa magoya bayansa kar su yarda da rigakafin saboda tana kisa.

A wani jawabi da sakataren yada labarai, Ifeanyi Emeka, ya fitar, kungiyar ta bayyana cewa; "mun yarda cewa gwamna Bello yana da 'yancin bayyana wautarsa amma ya sani cewa ba za'a zuba masa ido ya tsallake makadi da rawa ba, wautarsa ta tsaya iya kansa.

KARANTA: Hotuna: An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Teti, shekara 2,500 baya

"Sanyaya gwuiwar 'yan Nigeria akan karbar allurar rigakafin korona daidai yake da laifin yaki, saboda zai haddasa asarar rayuka."

An gargadi gwamna Yahaya Bello akan sukar allurar rigakafin cutar korona
An gargadi gwamna Yahaya Bello akan sukar allurar rigakafin cutar korona @Thecableng
Source: Twitter

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

"Sannan, babu wata allurar rigakafi da hukumar NAFDAC da ba zata duba inganci da sahihancinta ba kafin a fara amfani da ita.

"Mun san Yahaya Bello yana zagayen neman takarar shugaban kasa kuma bamu da wata damuwa akan hakan, amma ba zamu bari ya tunzura jama'a su ki shugaba Buhari ba saboda kawai yana son kujerarsa a 2023 ba, ba zamu yarda da haka ba.

Legit.ng ta rawaito cewa tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya ce zasu ƙirƙiro sabuwar tafiyar siyasa nan bada jimawa ba domin fatattakar manyan jam'iyyun Nigeria marasa manufa.

Okorocha ya bayyana hakan ne a ranar litinin, 18 ga watan Junairu 2021.

Tsohon gwamnan na jihar Imo a karkashin jam'iyyar APC ya ce PDP da APC sun kada ƴan Najeriya ƙasa wanwar

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel