Da duminsa: GMD na farko na NNPC, Festus Marinho ya mutu

Da duminsa: GMD na farko na NNPC, Festus Marinho ya mutu

- A ranar Talata shugaban NNPC na farko a Najeriya, Festus Marinho, ya koma ga Ubangiji

- Ya mutu yana da shekaru 87 a duniya bayan ya yi ayyuka tukuru wurin bunkasa matatu a Najeriya

- Marinho ne mutum na farko da ya rike kujerar shugabancin NNPC har sau biyu, daga 1977 zuwa 1979 da 1984 zuwa 1985

Festus Marinho, GMD na farko na NNPC, ya rasu a ranar Talata yana da shekaru 87. Marinho ne ya fara shugabantar NNOC, sannan ya shugabanci NNPC, The Cable ta ruwaito.

An haife shi a ranar 30 ga watan Disamban 1934 a Ijebu-Ode, kuma ya yi karatunsa a St. Gregory's College Obalende dake jihar Legas. Ya yi digirinsa na farko a bangaren Physics daga Jami'ar London a 1960.

Ya cigaba da karatu a Imperial College London inda ya karanta petroleum reservoir engineering daga 1960 zuwa 1961.

Shine kadai ya rike kujerar GMD na NNPC, wanda yayi a 1977 zuwa 1979 da kuma 1984 zuwa 1985. Lokacin yana shugabancin NNPC, ya kula da gine-gine, gyare-gyare da bunkasa matatu da bututun man fetur dake fadin Najeriya.

KU KARANTA: Hotuna: Ana saura kwana 3 daurin aure, uwargida ta kashe budurwar mijinta a Kano

Da duminsa: GMD na farko na NNPC, Festus Marinho ya mutu
Da duminsa: GMD na farko na NNPC, Festus Marinho ya mutu. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Bayan ya yi murabus, Marinho ya rike kujeru da matsayi iri-iri na sarauta, sannan ya samu jinjina da dama a bangarorin addini.

Ya kuma rike kujeru a ma'aikatun mayukan fetur, ciki har da shugabancin Lekoil Limited.

A wata takarda da shugaban NNPC na yanzu, Mele Kyari, ya gabatar wa da iyalan Marinho, ya kwatanta shi a matsayin "Uban ma'aikatun man fetur na Najeriya" sakamakon kokarinsa da dagewarsa wurin samar da cigaba ga ma'aikatu a cikin Najeriya da kasashen ketare da ake amfana dasu har yanzu.

"Hakika za a matukar yin kewar tarin iliminsa, kuma shi daya ne tamkar da goma."

KU KARANTA: Gumurzun 'yan bindiga da Zamfarawa: Mutum 10 sun mutu, an kone gidaje masu yawa

A wani labari na daban, jam'iyyar APC mai mulki ta musanta ikirarin jam'iyyar adawa ta PDP na cewa tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Dogara, wanda aka zaba domin wakilci a majalisar wakilai a zaben da ya gabata karkashin jam'iyyar PDP, ya koma jam'iyyar APC a shekarar da ta gabata.

Wannan musantawar ta jam'iyyar APC na dauke ne a wata takarda da ta mika gaban kotu wacce take martani ga PDP a gaban kotun bayan sun bukaci a kwace kujerar Dogaran.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel