Yakubu Dogara ba dan jam'iyyarmu bane, APC ta sanar da kotu

Yakubu Dogara ba dan jam'iyyarmu bane, APC ta sanar da kotu

- Jam'iyyar APC ta sanar da kotu cewa tsohon kakakin majalisa Dogara ba dan jam'iyyarta bane

- Shugaban fannin shari'a na APC, Oketade ya ce ya duba rijistar 'ya'yan jam'iyyar amma babu Dogara

- Hakan ya biyo bayan bukatar da PDP ta mika gaban kotu na son kwace kujerar Yakubu Dogara

Jam'iyyar APC mai mulki ta musanta ikirarin jam'iyyar adawa ta PDP na cewa tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Dogara, wanda aka zaba domin wakilci a majalisar wakilai a zaben da ya gabata karkashin jam'iyyar PDP, ya koma jam'iyyar APC a shekarar da ta gabata.

Wannan musantawar ta jam'iyyar APC na dauke ne a wata takarda da ta mika gaban kotu wacce take martani ga PDP a gaban kotun bayan sun bukaci a kwace kujerar Dogaran.

KU KARANTA: Hotuna: Ana saura kwana 3 daurin aure, uwargida ta kashe budurwar mijinta a Kano

Yakubu Dogara ba dan jam'iyyarmu bane, APC ta sanar da kotu
Yakubu Dogara ba dan jam'iyyarmu bane, APC ta sanar da kotu. Hoto daga @Thenation
Asali: UGC

Shugaban fannin shari'a na jam'iyyar APC, dare Oketade ya tabbatar da cewa bai san da labarin sauya shekar dogara ba zuwa jam'iyyar APC

Oketade ya ce ya duba rijistar 'ya'yan jam'iyyar APC kuma bai samu sunan Dogara ba, jaridar The Nation ta tabbatar.

KU KARANTA: An harbe mutum 1 bayan mutanen Kafanchan sun fito zanga-zanga kan karin kudin lantarki

A wani labari na daban, wani dan sanda mai mukamin sifeta ya rasu inda wasu suka raunata bayan harin da 'yan bindiga suka kai jihar Ribas, Channels Tv ta wallafa.

Hukumar 'yan sandan jihar Ribas ta ce kusan 'yan bindiga 17 ne suka kai gagagrumin hari kan jami'an 'yan sandan da aka tura Borikiri a Fatakwal a daren Lahadi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ribas, SP Nnamdi Omoni a wata takarda da ya fitar, ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Joseph Mukan ya bada umarnin zakulo wadanda suka aikata wannan laifin da gaggawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
APC