Hotuna: Ana saura kwana 3 daurin aure, uwargida ta kashe budurwar mijinta a Kano

Hotuna: Ana saura kwana 3 daurin aure, uwargida ta kashe budurwar mijinta a Kano

- 'Yan sanda jihar Kano sun cafke wata mata mai shekaru 20 da laifin kisan budurwar mijinta

- Suwaiba ta kashe Aisha ana sauran kwana uku daurin aurenta da mijinta Malam Shahrehu

- Suwaiba ta sanar da yadda ta ja Aisha wani kango sannan ta caka mata wuka a kirji, wuya da jiki

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wata matar aure mai shekaru 20 mai suna Suwaiba Shuaibu a kan zarginta da sokawa wata Aisha Kabir wuka ana sauran kwanaki kadan aurenta.

An gano cewa Aisha ce wacce Malam Shahrehu Alhaji Ali, mijin wacce ake zargin zai aura a ranar 9 ga watan Janairu a kauyen Gimawa, karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano, Daily Trust ta wallafa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata, ya ce an nema amaryar an rasa amma daga baya sai aka ga gawarta a wani kango.

Hotuna: Ana saura kwana 3 daurin aure, uwargida ta kashe budurwar mijinta a Kano
Hotuna: Ana saura kwana 3 daurin aure, uwargida ta kashe budurwar mijinta a Kano. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Kamar yadda takardar tace: "A ranar 2 ga watan Janairu wurin karfe 10:30 na safe mun samu labarain ganin gawar Aisha Kabir daga kauyen Gimawa a wani kango.

"Mai korafin ya ce ana zargin an soka mata wuka ne a wuya. Mun ziyarci wurin inda muka dauka gawarta zuwa babban asibitin Tudun Wada wanda likita ya dubata.

"Kwamishinan 'yan sanda CP Habu A. Sani ya bukaci jami'an tsaro da su nemo wadanda suka yi aika-aikar.

"A wannan halin ne aka damko Suwaiba Shuaibu mai shekaru 20. Bincike ya nuna cewa mijinta ya kashe shekaru 6 suna soyayya da budurwar kuma za su yi aure."

KU KARANTA: Hotunan ministan Buhari yana yawo da sandar guragu sun janyo cece-kuce

Kiyawa ya ce wacce ake zargin ta amsa laifinta. Ta ce da kanta ta kira budurwar mijinta sannan ta kaita kangon ta soka mata wuka a wuya, kirji da sauran sassan jikinta.

Ya ce an mika lamarin hannun sashin bincike na musamman kan kisan kai kuma za a mika wacce ake zargin a gaban kotu.

KU KARANTA: 2023: Wallafa hoton El-Rufai da Tinubu ya janyo wa Bashir El-Rufai mugun zagi daga jama'a

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Lahadi ya gabatar da motocin alfarma biyu ga sabon Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Elkanemi domin saukaka masa tafiye-tafiye da al'amuran mulkinsa.

Daya daga cikin motocin akwai kirar SUV Lexus ta 2020 sai wata kirar Toyota Hilux ta 2020.

Babban sakatare a ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu, Tarfaya Asariya, wanda ya samu rakiyar kwamishinan ayyukan noma, Injiniya Bukar Talba ne suka mika motocin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel