Gumurzun 'yan bindiga da Zamfarawa: Mutum 10 sun mutu, an kone gidaje masu yawa

Gumurzun 'yan bindiga da Zamfarawa: Mutum 10 sun mutu, an kone gidaje masu yawa

- Akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai jihar Zamfara

- 'Yan bindigan sun kai farmaki kauyen Talli, Dutsin Gari da Rayau a Kanoma dake karamar hukumar Maru

- Sun kashe manyan shugabannin 'yan sa kai dake kauyakun sannan sun kai farmaki gidaje da dama dake kauyakun

Mutane akalla 10 ne suka rasa rayukansu da gidajensu bayan 'yan bindiga sun kai wa 'yan kauyen Talli, Dutsin Gari da Rayau dake karamar hukumar Maru a jihar Zamfara farmaki, kamar yadda Daily trust ta ruwaito.

Mazauna garin sun sanar da manema labarai cewa wasu 'yan bindiga sun je Dutsen Gari a baburansu da niyyar su yi garkuwa da mazauna garin, ba su san 'yan kauyen suna da cikakken shirinsu ba.

Take a nan aka fara musayar wuta tsakanin 'yan bindigan da 'yan kauyen wanda aka yi sa'o'i da dama ana yi. Bayan ganin ba za su samu nasara ba 'yan bindigan suka tsere daga kauyen.

KU KARANTA: Hotuna: Ana saura kwana 3 daurin aure, uwargida ta kashe budurwar mijinta a Kano

Gumurzun 'yan bindiga da Zamfarawa: Mutum 10 sun mutu, an kone gidaje masu yawa
Gumurzun 'yan bindiga da Zamfarawa: Mutum 10 sun mutu, an kone gidaje masu yawa. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

'Yan bindigan sun zarce kauyen Rayau, a can inda suka yi artabu da mazauna wurin.

"Yan bindigan sun kashe manyan shugabannin 'yan sa kan kauyen sannan sun tsere da dabbobi da dama. Basu tsaya anan ba, sai da suka tattaba gidajen wadanda suka tsere saboda tsoron zuwansu kauyen," kamar yadda wani mazaunin yankin yace.

Ba a samu jin ta bakin kakakin 'yan sandan yankin ba, Muhammad Shehu, yayin tattara bayanai.

Sai dai wani ganau ya shaida wa BBC cewa sun tsere cikin dajika don tsoron 'yan bindigan su harbesu. Amma sun kashe fiye da mutane 10.

A cewarsa, sun samu nasarar tattaro gawawwaki 7, amma sai sun shiga daji tukunna za su nemo sauran. Sannan sojoji sun je bayan harin, amma ba su yi komai ba akai.

Kwamishinan harkokin cikin gida da na tsaro na jihar Zamfara, Abubakar Dauran, ya ce ya tura jami'an tsaro wurin da lamarin ya faru, yanzu haka yana jiran ji daga garesu ne.

KU KARANTA: Bidiyon yaro yana kuka bayan mahaifiyarsa ta ce ba za ta aure shi ba ya nishadantar

A wani labari na daban, fusatattun matasan Kafanchan sun bi titin gidan man Ernmaco zuwa ofishin wutar lantarki na Kaduna suna zanga-zanga akan tashin kudin wuta da kuma rashin samun wutar lantarki yadda ya dace.

Mazauna yankin, wadanda yawanci matasa ne, sun isa har ofishin wutar lantarkin dake Kafanchan rike da takardu wadanda aka rubuta, "A daina amsar kudade masu yawa daga hannunmu, muna bukatar isasasshiyar wuta, a daina barinmu a cikin duhu".

Yayin da Daily Trust ta je wurin an harbi wani dalibin GSS Takau dake Kafanchan, mai suna Noah Ransom a bayansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng