Hadimar gwamna tayi murabus domin tsiratar da aurenta, ta mika wasikar ajiye aiki

Hadimar gwamna tayi murabus domin tsiratar da aurenta, ta mika wasikar ajiye aiki

- Hadimar Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ta rubuta wasikar ajiye aiki zuwa ga gwamnan

- Hadimar gwamnan kan ci gaban kasuwanci, Deaconness Emerald Udeakaji, ta bayyana matsalar gidanta a matsayin abunda yasa tayi murabus daga gwamnatin

- A wasikar murabus din nata, ta ce ta yi murabus ne don tsiratar da aurenta wanda ke barazanar tarwatsewa

A wani yunkuri na bazata, wata hadimar Gwamnan jihar Ebonyi tayi murabus daga gwamnatin.

Hadimar wacce kafin murabus dinta take a matsayin babbar mai bayar da shawara ga gwamnan kan ci gaban kasuwanci ta bayyana dalilinta na ficewa daga gwamnatin.

A wasikar murabus dinta mai kwanan wata Laraba, 30 ga watan Disamba, 2020, wanda Legit.ng ta gano, Deaconness Udeakaji ta bayyana cewa murabus din nata ya zama dole domin tsiratar da aurenta.

Hadimar gwamna tayi murabus domin tsiratar da aurenta, ta mika wasikar ajiye aiki
Hadimar gwamna tayi murabus domin tsiratar da aurenta, ta mika wasikar ajiye aiki Hoto: Newsline9ja.com
Source: UGC

Ta riki cewa a lokacin da take yiwa jihar hidima, ta yi biyayya ga gwamnatin dari bisa dari, amma a yanzu ana magana ne a kan iyalinta.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: FG tayi amai ta lashe, ta ce bata yarda da bude makarantu a ranar 18 ga Janairu ba

Wasikar da ta aikewa Gwamna Umahi ya zo kamar haka:

“Ina mika godiya ga mai girma Gwamna, matarsa da ahlin Umahi a kan damar da suka bani don yin aiki a wannan gwamnatin.

“Nagode sosai yallabai. Na ajiye aiki ne saboda matsalolin gidana. Na yi biyayya ga wannan gwamnati dari bisa dari amma gidana na tarwatsewa.

“Littafin Injila ya ce , ‘mace ta zamo mai sadaukarwa ga mijinta’. A matsayina na mai hidima, ya zama dole na koma na kuma yi nazarin littafina mai tsarki sosai. Domin biyayya ga wannan littafin mai tsarki, na yanke shawarar yin murabus da ceto aurena.

“Ina matukar godiya a kan dukkan abubuwan da kuka yi mun. Ni ba butulu bace kuma ba zan taba zama butulu ba. Dan Allah kuyi hakuri dani saboda yarana. Ina maka fatan alkhairi a harkokin siyasarka na gaba. Nagode, ya mai girma kuma ka ci gaba da kasancewa cikin aminci."

KU KARANTA KUMA: Abunda yasa akwai bukatar yan Nigeria su marawa shugabancin Tinubu baya a 2023, dan majalisa ya bayyana dalilai

A wani labari na daban, manyan jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun shawarci Gwamna Yahaya Bello da Gwamna David Umahi a matsayin mafi kyawun 'yan siyasa da zasu mulki Najeriya a 2023.

Shawarwarin sun fito ne daga kakakin majalisar dokokin Kogi, Mathew Kolawole, da takwaransa na majalisar Ebonyi, Francis Nwifuru.

Duk mutanen biyu a wajen taron siyasa a jihar Ebonyi sun yi ikirarin cewa Bello da Umahi suna da kwarewar da ake bukata don shugabancin kasar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel