Abunda yasa akwai bukatar yan Nigeria su marawa shugabancin Tinubu baya a 2023, dan majalisa ya bayyana dalilai
- Ya kamata a bari Bola Tinubu yayi takarar shugaban kasa, a cewar wani dan majalisa daga Badagry
- Babatunde Hunpe ya ce jigon na APC ya sauke dukka hakokinsa na siyasa a kasar
- Ya kara da cewa Tinubu na son Najeriya kuma ci gaban kasar shine abu mafi muhimmanci a gare shi
An bukaci yan Najeriya da su marawa takarar Asiwaju Bola Tinubu baya a zaben shugaban kasa na 2023.
Babatunde Hunpe, dan majalisa mai wakiltan mazabar Badagry a majalisar wakilai ne yayi wannan kiran a ranar Litinin, 18 ga watan Janairu.
Ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Badagry.
KU KARANTA KUMA: CAN ga Zulum: Kiristoci basa ta’addanci, Boko Haram sun bayyana akidarsu
A cewarsa, Tinubu ya sauke hakokinsa ta fuskacin siyasa a kasar.
Ya ce:
“Muna yin wannan ne saboda ra’ayin kanmu, amma wannan ba shine mafi ahla ba domin ba zai iya kaimu koina ba.
“Tinubu ya sauke hakkokinsa, ya yi wa kasar hidima sosai, kuma idan mutumin ya fito cewa yana son kowani abu, ina so na roki dukkanin yan Najeriya a kan su mara masa baya.”
KU KARANTA KUMA: COVID-19: FG ta ce akwai yiwuwar sake kulle kasar a karo na biyu, ta gargadi yan Nigeria
Da yake ci gaba, ya ce jigon na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya yiwa Najeriya tanadi mai kyau a zuciyarsa.
A wani labarin, mun ji cewa a ranar Litinin, 18 ga watan Junairu, 2021, aka ji Sanata mai wakiltar yammacin jihar Imo, Rochas Owelle Okorocha, ya na kara sukar jam’iyyar APC.
Jaridar Punch ta rahoto Sanata Rochas Okorocha yana cewa anyi gaggawan kafa jam’iyyar APC da nufin ta karbe mulki daga hannun PDP a zaben 2015.
Tsohon gwamnan na jihar Imo, ya bayyana cewa shi da wasu ‘yan siyasa masu tunani irin na sa, suna yunkurin kafa wata sabuwar tafiyar siyasa a kasar.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng