COVID-19: FG tayi amai ta lashe, ta ce bata yarda da bude makarantu a ranar 18 ga Janairu ba

COVID-19: FG tayi amai ta lashe, ta ce bata yarda da bude makarantu a ranar 18 ga Janairu ba

- FG ta bayyana cewa bata amince da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi ba kan komawa makarantu a ranar 18 ga watan Janairu

- Wasu makarantu a fadin Najeriya sun koma harkokin karatu a ranar Litinin, 18 ga watan Janairu

- Sai dai kuma, ministan ilimi Adamu Adamu, ya bayyana cewa za a sake duba batun komawa makarantun

Gwamnatin tarayya a ranar litinin, ta ce tana adawa da batun komawa makarantu a ranar 18 ga watan Janairu.

A wajen taron tattaunawa na kwamitin fadar shugaban kasa kan korona, ministan ilimi, Adamu Adamu, ya ce gwamnatin tarayyar bata amince da matsayar jihohi kan ranar komawa makaranta ba.

Adamu, wanda ya bayyana cewa PTF za ta lura da yanayin korona a kulla yaumin, ya ce ana iya sake duba batun ranar komawa makarantu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

COVID-19: FG tayi amai ta lashe, ta ce bata yarda da bude makarantu a ranar 18 ga Janairu ba
COVID-19: FG tayi amai ta lashe, ta ce bata yarda da bude makarantu a ranar 18 ga Janairu ba Hoto: @DigiCommsNG
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Abunda yasa akwai bukatar yan Nigeria su marawa shugabancin Tinubu baya a 2023, dan majalisa ya bayyana dalilai

“Mun zauna, mun duba alkaluman sannan muka yanke shawarar cewa kada a bude makarantu.

“Abun bakin ciki, ya zama dole mu bayyana wannan saboda ya kamata ace ya zama hukuncin bai daya, amma ya zama dole ku fahimci cewa maganar makarantu ake yi, gwamnatin tarayya na da kimanin makarantu 100 ne kawai cikin dubban makarantu.

“Makarantun na karkashin ikon jihohi ne kuma yayinda PTF ta ce hada kai wajen cewa kada a bude makarantu, jihohi sun hade cewa a bude makarantu.

“Don haka, ya zama dole mu sasanta sannan a matsayinmu na PTF za mu lura da abubuwan da ke faruwa a kulla yaumin. Ana iya sake duba lamarin,” in ji Adamu.

KU KARANTA KUMA: CAN ga Zulum: Kiristoci basa ta’addanci, Boko Haram sun bayyana akidarsu

A gefe guda, Gwamnatin tarayya ta bukaci yan Najeriya da su yi duk abunda za su iya don guje ma rufe Najeriya a karo na biyu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban kwamitin fadar shugaban kasa kan korona, Boss Mustapha ne yayi wannan rokon a ranar Litinin, 18 ga watan Janairu, a wani taron manama labarai.

Legit.ng ta tattaro cewa Mustapha, wanda ya kuma kasance sakataren gwamnatin tarayya, ya ce hakan zai kasance ne ta hanyar bin ka’idojin da gwamnati ta saki.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel