EFFC ta sake gurfanar da Mama Boko Haram bisa sabon zargin Naira miliyan 1.7

EFFC ta sake gurfanar da Mama Boko Haram bisa sabon zargin Naira miliyan 1.7

- An gurfanar da Mama Boko Haram bisa tuhumar damfarar kudi Naira miliyan 41

- An gurfanar da Mama Boko Haram tare da wasu karin mutane biyu sai dai sun karyata tuhumar da ake musu

- Kotu ta dage sauraren karar tare da bawa wanda ake tuhumar damar daukar Lauyan da zai kare su

Hukumar yaki da rashawa ta EFFC, ta gurfanar da Aisha Alkali Wakil wanda aka fi sani da 'Mama Boko Haram' a gaban Mai shari'a Aisha Kumaliya ta babbar kotun Jihar Borno da ke zamanta a Maiduguri, a bisa sabbin tuhume tuhume guda uku da suka hada da damfarar kudi har N41,777,750.

An gurfanar da Mama Boko Haram tare da Tahiru Saidu Daura, da Prince Lawal Shoyede, shugabannin Complete Care and Aid Foundation (wata kungiyar sa kai).

EFFC ta sake kama Mama Boko Haram bisa sabon zargin miliyan 41.7
EFFC ta sake kama Mama Boko Haram bisa sabon zargin miliyan 41.7. Hoto: @daily_nigerian
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya amince da nadin Nuhu Fikpo a matsayin shugaban riko na NDE

A wata sanarwa da shugaban yada labaran EFFC, Wilson Uwujaren ya fitar, wanda ake tuhumar ana zargin su da damfarar wata Hajia Bilkisu Mohammed Abubakar akan kwangilar da ta haura miliyan 41 ga gidauniyar Complete Care and Aid Foundation, mallakar Wakil, amma suka ki biya.

Daya daga cikin tuhumar: "ke Aisha Alkali Wakil, Tahiru Saidu Daura da Prince Lawal Shoyede a matsayin shugabannin Complete Care and Aid Foundation (kungiyar sa kai) wasu lokuta a shekarar 2018 a Maiduguri, Jihar Borno a wannan kotu mai albarka, ana tuhumar ku da ha'intar wata Hajia Bilkisu Mohammed Abubakar ta Ihsan Vendor Services, da ta kawo muku kayan dakin gida, kayan wuta da kayan abinci na fiye da N34,593,000 (miliyan 34 da dubu dari biyar da 33) tare da umartar a kai kayan gidan shugaba/wanda ya samar da gidauniyar Complete Care and Aid Foundation(kungiyar sa kai) Aisha Alkali Wakil, laifin da ya sabawa sashe na 320 (a) kuma aka tanadi hukunci a sashe na 322 na kudin Penal Code na Jihar Borno."

KU KARANTA: Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ya mutu kwanaki 10 bayan rasuwar matarsa

Sai dai wanda ake zargin sun karyata tuhumar da ake musu.

A dalilin haka, lauyan masu kara, Haruna Abdulkadir, ya bukaci kotu ta saka ranar sauraron shaidu, don bawa wanda ake karar damar daukar lauya.

Mai shari'a Kumaliya ya dage sauraren karar zuwa 26 ga Janairu 2021 tare da umartar 'Mama Boko Haram' da Shoyede da su dauki lauya, ko kuma aci gaba da sauraren karar da EFFC ta shigar ba tare da lauya mai kare su ba.

A wani labarin daban, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Jihar Kebbi ta ce tana fatan za ta kwace mulki daga All Progressives Congress (APC) a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban jam'iyyar na jihar, Haruna Sa'idu, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin da ya ke tarbar jigo a jam'iyyar APC, Abdulmalik Halliru Milton, wadda ya fice daga APC ya koma PDP a Birnin Kebbi.

Sai'idu, ya kuma soki yan majalisar dokokin jihar da ya ce suna bari gwamnan Jihar Abubakar Atiku Bagudu na juya su duk yadda ya so.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel