Buhari ya amince da nadin Nuhu Fikpo a matsayin shugaban riko na NDE
- Shugaba Buhari ya tabbatar da nadin Abubakar Nuhu Fikpo a matsayin shugaban hukumar NDE
- Sanarwar ta fito ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa Bashir Ahmad da safiyar yau Litinin
- A watan da ya gabata ne shugaba Muhammadu Buhari ya soke nadin tsohon shugaban hukumar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mallam Abubakar Nuhu Fikpo a matsayin sabon shugaban hukumar samar da aikin yi na kasa, NDE.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da karamin ministan aiki da kwadago, Festus Keyamo, SAN, mai kwanan wata 18 ga Janairu 2021 kamar yadda hadimin shugaban kasa Bashir Ahmad ya sanar a Twitter.
DUBA WANNAN: Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ya mutu kwanaki 10 bayan rasuwar matarsa
KU KARANTA: Jami'an tsaro sun yi awon gaba da Almajiran Dahiru Bauchi a Kaduna cikin dare
A wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Bashir Ahmad ya fitar ya ce, "Shugaba Buhari ya aikewa da karamin ministan kwadago, Mr. Festus Keyamo, SAN, takardar amincewa da nadin Mallam Abubakar Nuhu Fikpo a matsayin sabon shugaban hukumar NDE a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon shugaban hukumar."
Sanarwar ta tuno da shugaba Buhari ya cire tsohon shugaban hukumar a watan da ya gabata tare da umartar ministan da ya nada daya daga cikin daraktocin hukumar a matsayin shugaba kafin daga bisani a tabbatar da nadin a matsayin shugaban hukumar.
A wani labarin daban, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Jihar Kebbi ta ce tana fatan za ta kwace mulki daga All Progressives Congress (APC) a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban jam'iyyar na jihar, Haruna Sa'idu, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin da ya ke tarbar jigo a jam'iyyar APC, Abdulmalik Halliru Milton, wadda ya fice daga APC ya koma PDP a Birnin Kebbi.
Sai'idu, ya kuma soki yan majalisar dokokin jihar da ya ce suna bari gwamnan Jihar Abubakar Atiku Bagudu na juya su duk yadda ya so.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng