Za mu kayar da APC a Kebbi, in ji shugaban PDP

Za mu kayar da APC a Kebbi, in ji shugaban PDP

- Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, reshen Jihar Kebbi ta ce tana dab da kwace mulki daga hannun APC

- Shugaban PDP na jihar, Haruna Sa'idu ne ya bayyana hakan yayin tarbar jigon APC na jihar Halliru Milton da ya koma PDP

- Sa'idu ya ce ficewar manyan yan siyasa kamar Milton daga jam'iyyar alama ce da ke nuna jam'iyyar bata yi wa al'umma aiki

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Jihar Kebbi ta ce tana fatan za ta kwace mulki daga All Progressives Congress (APC) a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban jam'iyyar na jihar, Haruna Sa'idu, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin da ya ke tarbar jigo a jam'iyyar APC, Abdulmalik Halliru Milton, wadda ya fice daga APC ya koma PDP a Birnin Kebbi.

Za mu kayar da APC a Kebbi, in ji shugaban PDP
Za mu kayar da APC a Kebbi, in ji shugaban PDP. @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tsohon ministan Nigeria, Jubril Kuye ya riga mu gidan gaskiya

Ya ce, "Idan manyan yan siyasa kamar Milton, wanda suka taimakawa APC ta samu mulki a jihar, sun fara dawowa PDP, hakan na nufin cewa PDP tana daf da karbe mulki daga APC da bata tabuka komai a jihar."

Sai'idu, ya kuma soki yan majalisar dokokin jihar da ya ce suna bari gwamnan Jihar Abubakar Atiku Bagudu na juya su duk yadda ya so.

"Dukkan mu mun ga faifan bidiyon da ya bazu a dandalin sada zumunta inda wani jigo a APC ya soki gwamnatin APC na jihar saboda rashin tabbuka aiki. Don haka, mu jam'iyyar PDP ta kowa ce. Muna maraba da duk wanda ya ke shirin shigowa jam'iyyar. Ina kuma kira gareku ku cigaba da janyo mana wasu su shigo jam'iyyar," in ji shi.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun ceto mutum 8 daga hannun masu garkuwa, sun kama mutum 22

A jawabinsa, Milton ya ce ficewa daga APC ya koma PDP na cikin muhimman matakan da ya dauka a baya bayan nan, ya kara da cewa gwamnatin APC mai ci yanzu an gina ta kan yaudara ne sannan bata tubuka komai duba da yadda mutane ke rayuwa cikin mawuyacin hali.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164