Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ya mutu kwanaki 10 bayan rasuwar matarsa

Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ya mutu kwanaki 10 bayan rasuwar matarsa

- Jerome Eke, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ya mutu kwanaki kadan bayan rasuwar matarsa

- Eke ya wakilci mazabar Etche/Omuma a Majalisar Wakilan Tarayya karkashin jam'iyyar PDP daga shekarar 2015 zuwa 2019

- Ogbonna Nwuke, magajinsa a Majalisar Wakilai ta Tarayya ya tabbatar da rasuwarsa inda ya ce mutumin kirki ne

Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Jerome Eke, ya rasu kwanaki kadan bayan mutuwar matarsa mai suna Joan, The Punch ta ruwaito.

Eke ya wakilci mazabar Etche/Omuma a Majalisar Wakilai na Tarayya karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party daga shekarar 2015 zuwa 2019.

Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ya mutu kwanaki 10 bayan rasuwar matarsa
Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ya mutu kwanaki 10 bayan rasuwar matarsa. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Za mu kayar da APC a Kebbi, in ji shugaban PDP

An ruwaito cewa tsohon dan majalisar na tarayya ya rasu a ranar Juma'a, kwanaki 10 bayan rasuwar matarsa duk da cewa ba a sanar da sanadin mutuwarsa ba.

Da aka tuntube shi, wanda ya maye gurbinsa a majalisar wakilai, Ogbonna Nwuke ya tabbatar da rasuwar dan majalisar.

Nwuke, wanda shine kakakin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Rivers ya bayyana Eke a matsayin "mutum mai basira da halaye na gari", inda ya ce rasuwarsa babban rashi ne ga mutanen Etche.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace matafiya a Omo-Ijesa

"Shi (Eke) mutumin kirki ne kuma mai basira sannan muna da alaka mai kyau duk da banbancin siyasarmu. Babban rashi ne ga al'ummar Etche," in ji Nwuke.

Kazalika, kansila kuma shugaban Etche Legislative Assembly, Blackson Nwayanwu ya ce, "Eh, shi (Eke) ya rasu. Amma ban san ainihin yadda abin ya faru ba. Matarsa ma ta rasu."

A wani labarin daban, lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN a ranar Laraba ya tunkari kotu don janye karar da wanda ya ke karewa ya shigar.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Bashar wanda ya rasu ranar Juma'a, 1 ga Janairu, 2021, Daily Trust ta ruwaito.

Ustaz a wata tattaunawa ta wayar hannu da Daily Trust ranar Laraba ya ce ya bukaci janye karar wanda aka yi nan take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164