2023: Tsohon gwamnan Kano ya bukaci arewa da ta mutunta tsarin mulkin karba-karba
- Sanata Kabiru Gaya ya nuna muradinsa na son ganin yankin kudancin kasar ta samar da Shugaban kasar Najeriya a 2023
- Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce shine abunda ya kamata ayi ta fuskacin hada kan kasar
- Ya yi kira ga yan siyasan arewa da su mutunta tsarin mulkin karba-karba don muradin kasar
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan hukumar zabe (INEC) mai ci, Sanata Kabiru Gaya ya nuna muradinsa na son ganin yankin kudancin kasar ta samar da Shugaban kasar Najeriya na gaba.
Sanatan mai wakiltan Kano kudu ya bayyana cewa idan shugaba Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa na shekaru takwas a 2023, zai zama rashin adalci idan arewa ta nemi kujerar Shugaban kasar kuma.
KU KARANTA KUMA: Zazzafan martani daga yan Nigeria yayinda Buhari ya saki tantabaru amma suka ki tashi a wajen tunawa da sojoji
Ya yi martanin ne a wata hira da jaridar Daily Sun wanda aka wallafa a ranar Asabar, 16 ga watan Janairu.
Martaninsa:
“Muna maganar Najeriya daya da hada kan wannan kasar kuma idan kana ganin cewa arewa na da ikon zama Shugaban kasa, hakan ba yana nufin kaine za ka ta yin Shugaban kasa a dukkan lokaci ba, ya kamata mu bari abun ya dunga zagaye harma ga yankunan da basu da rinjay, ya kamata mu basu damar shugabantar kasar da hada kanmu.”
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Kaduna ta ce ta ceto yaran Almajirai 160 a Kaduna
Ya bayyana cewa har sai Najeriya ta samu hadin kai, kasar ba za ta cimma muradinta ba a matsayin kasa.
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kasar za ta samu gagarumin ci gaba a lamarin tsaro a 2021.
A wasu jerin wallafa da yayi don raya ranar tunawa da sojoji, Shugaban kasar ya bukaci shugabannin tsaro da su tabbatar da hada hannu wajen yaki da rashin tsaro.
Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ba jin dadin rundunar sojin muhimmanci.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng